Kaduna Marathon: Ɗan Kenya ya samu kyautar miliyan huɗu a gasar tsere ta Jihar Kaduna

Asalin hoton, @KadunaMarathon
Ɗan ƙasar Kenya John Muiruri Mburu ne ya zama zakara a gasar gudun famfalaƙi ta duniya da ake yi a Kaduna ɓangaren tseren kilomita 21, a cewar rahoton shafin kick442.com.
An ƙaddamar da gasar ce mai suna Kaduna Marathon, wadda ta ƙunshi ajin tseren kilomita 10km da 5km da kuma 21kma, a yau Asabar.
An bai wa John Mburu dala 10,000 (kwatankwacin kusan naira miliyan huɗu) a matsayin kyautar zama zakara.

Asalin hoton, @KadunaMarathon
A sauran azuzuwan gasar, Mohammed Sani Musa na Kaduna ne ya lashe gasar gudun kilomita 5km.
Ita kuma Kangyang Solomon ta Jihar Filato ta lashe ɓangaren mata na gudun kilomita 10km, yayin da ɗan shekara 15 Gyang David ya lashe tserensa na farko a matakin ƙasa.
Shugaban ƙungiyar wasan ƙwallon Volleyball ta Najeriya, Injiniya Musa Nimrod wanda ya halarci gasar, ya yaba wa gwamnatin Jihar Kaduna da Nilayo Sports game da yadda suka shirya gasar.
Wasu daga cikin manyan 'yan wasan guje-guje da tsalle-tsalle da suka fafata sun haɗa da Shehu Mu'azu da Ismael Sadjo da kuma Danjuma Gyang.
Kusan mutum 7,000 ne suka nemi shiga gasar ta Kaduna Marathon 2020.
Gwanayen da suka fito daga ƙasashe irin su Kenya da Kamaru da Habasha da dai sauransu, na cikin shauƙi da farin cikin wannan gasa da za a samu kyaututtuka.
Sai dai an gudanar da wannan gasar a dai-dai lokacin da al'ummomi ke nuna damuwa kan taɓarɓarewar sha'anin tsaro a Kaduna.
To sai dai kwamishina mai kula da harkokin wasanni na jihar, Farfesa Kabiru Mato, ya ce gwamnatin jihar na daukar matakai na kare rayuka da dukiyoyin jama'a.
Maƙasudin gasar
Gwamna Nasir Elrufai ya ce gwamnati ta shirya wannan gasa ce domin nuna wa duniya irin albarkatunta a fannin yawon buɗe ido da kuma bai wa ƴan kasa damar motsa jikinsu.
Sannan akwai bukatar jaddada ko karfafa hadin-kai da zaman lafiya tsakanin al'umomi, kuma gasa irin haka na habbaka tattalin arziki da taimaka wa matasa, da kuma zaburar da mutane kan kula da lafiya, in ji gwamnan.
Gwamnan ya kuma kara da cewa za a samu shigowar baƙi daga sassa daban-daban na duniya domin yawon buɗe ido.
Elrufai ya nemi haɗin-kan ƴan jihar domin ganin an gudanar da gasar cikin raha da anashuwa, da kuma ƙarfafa gwiwar masu shiga tseren da jami'ai.
Ya gasar za ta gudana?
Gwamnatin Kaduna dai ta tabbatar da cewa akwai mutane sama da 80 da suka gwanance a gudu ƴan Najeriya da za su shiga gasar.
An kuma rarraba yadda za a gudanar da gasar zuwa gida uku, akwai rukunin ƴan tseren kilomita 21 da masu yin kilomita 10 da kuma kilimota 5 a bangaren maza da kuma mata.
Sannan gwamnati ta sanar da cewa za a rufe wasu tituna cikin garin Kaduna daga karfe 6.00am na safe zuwa 3.00pm na yamma domin tabbatar da tsaro da nasarar gasar.











