'Satar fasaha ka iya sanadin karyewar 'yan Kannywood'

Kannywood

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Jabir Mustapha Sambo
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa, Abuja

Satar fasaha na daya daga cikin abubuwan da suka dade suna ciwa masana'antar Kannywood tuwo a kwarya. Hakan ta sa jama'a da dama musamman masu ci a karkashin masana'antar fina-finan ke fargabar cewa satar fasaha na dab da ruguza ta ga baki daya.

Shekaru da dama da su ka gabata masana'antar Kannywood ta fantama sosai ta fuskar samun kudaden shiga, kama daga lokacin da a ke rububin sayen fina-finan su a kaset din bidiyo, kafin a ka fara yayin faifan CD har ma da lokacin da zamanin amfani da DVD ya shigo.

To sai dai yayin da masa'antar ke tsakiyar shanawa, kwatsam sai ga al'adar satar fasaha ta shigo. Kuma sannu a hankali ta samu gindin zama, har a yanzu ta ke neman ruguza masana'antar da dubbai ke cin abinci a karkashinta.

Usman Mua'zu na daya daga cikin masu shirya fina finan a wannan Masana'anta,kuma ya fadawa BBC cewa ya shafe shekaru yana ci a karkashin wannan sana'a. To amma a cewarsa satar fasaha ta sa jikinsa ya fara sanyi, lura da irin asarar da ta sa su ka tabka da a cewarsa ba ta misaltuwa.

"Ba karamar asara mu ke yi ba.I dan zan buga maka misali da ni kaina, yanzu haka ina da fina-finai akalla guda uku da na kashe kusan miliyan bakwai wurin shirya su. To amma tsoron satar fasaha ya sa na kasa sakin su kasuwa. Ina tsoron idan na sake su ko kudin da na kashe ba zan mayar ba ballantana inyi tunanin samun riba."

Matsalar satar fasaha ba masu shirya fina finan kawai ta taba ba, matsala ce da ta zama bulaliyar kan hanya , domin ko ta shafi su kan su masu dillancin fina finan.

Sani Al Rahuz na daya daga cikin masu dillancin fina finai a masana'antar fina-finan ta kannywood, kuma mamallakin kamfanin Al-Rahuz films production. Kamar yadda ya shaida wa BBC kasuwar fina-finan ta samu asarar kusan kashi casa'in cikin dari na abinda ta ke samu a shekarun baya.

"A da na shirya fim na miliyan bakwai har ma miliyan takwas. Kuma yanzu ina kan shirya fim da zai lakume naira miliyan 15. 'To amma saboda lura da yadda satar fasaha ke dada gurgunta Kannywood dole ta sa nayi watsi da aikin.

An yi lokacin da na buga fim kwafi 500,0000 kuma duka na sayar da su, amma a yanzu ban san wata kasuwa ba a duk fadin Najeriya da zan iya sayar da kwafi dubu 10 kacal". In ji Sani Al-Rahuz.

Yayin da masu shirya fina finan da masu dillanci ke kuka da satar fasaha, taurari a masana'antar ta Kannywood sun ce ai su ne da kuka, la'akari da cewa matsawar a ka gagara shirya fim, to su kuma kasuwarsu ta zo karshe.

A tabakin tauraruwa Halima Yusuf Atete, masu satar fasaha na cin karen su ba bu babbaka ne da goyon bayan al'umma.

'Duk lokacin da zamani ya sauya muna sauyawa.Amma a wannan karon masu satar fasaha saboda rashin adalcinsu, za a shirya a kuma buga fim, sai su samu kwafi daya su sauke a kwafyuta suna turawa jama'a a kan kudi naira 30 ko naira 50.Kaga wannan ba adalci bane'.

To sai dai a cewar Halima Yusuf Atete 'jama'ar da a da ke sayen faifan CD kuma su ne ke zuwa a na tura musu a waya wanda hakan ya sa su ka daina sayen fim.

"To ka ga babu yadda za'a yi masu shirya fina finai su rika shirya fim suna tabka asara.Idan kuma ba a shirya fim din ba mu taurari kasuwar mu ta samu matsala."

Kannywood

Asalin hoton, Kannywood

Wannan layi ne

Da yawa a Kannywood na ganin gwamnati ta taimaka wurin ci gaban satar fasaha, lura da cewa suna biyan haraji ga hukumomi don kare musu abincinsu, to amma humumomin ba sa yin aikinsu.

BBC ta yi iya kokarin jin martanin hukumar da ke yaki da satar fasaha a Najeriya kan zargin nuna gazawa wurin dakile satar fasahar, to amma har kawo lokacin fitar da wannan rahoto sun ki su ce komai.

To sai dai BBC ta tattauna da wani mai sana'ar satar fasahar wanda ya nemi a sakaya sunansa, kuma ya shaida wa BBCn cewa rayuwarsa ta sauya sosai da wannan sana'a.

A cewarsa "da wannan sana'a na mallaki gida da abin hawa har ma na ke taimakawa yan uwa da abokan arziki, kuma yanzu haka matasa hudu ke cin abinci a karkashi na."

A daidai lokacin da al'umma a Najeriya musamman matasa ke kukan rashin aikin yi, durkushewar masana'antar fina-finai ta Kannywood a irin wannan lokaci zai dada dagula al'amura musamman a arewacin kasar.