Kasuwar cinikin 'yan ƙwallon ƙafa: Makomar Ronaldo, Sterling, Jesus, Nunez, Romero, Giroud

Cristiano Ronaldo

Asalin hoton, Elma

Manchester City na shirin sabunta kwangilar dan wasan Ingila Raheem Sterling, mai shekara 25, a cewar jaridar (Sunday Mirror).

Kazalika City ta duƙufa wajen ganin ta inganta albashin dan wasan Brazil Gabriel Jesus, mai shekara 23, inda zai rika samun £150,000 duk mako. (Star on Sunday)

KocinManchester City Pep Guardiola ya mayar da hankali wajen neman dan wasan da zai maye gurbin dan kasar Argentina Sergio Aguero, mai shekara 32, kuma ana tunanin zai dauko dan wasanBenfica dan kasar Uruguay Darwin Nunez, mai shekara 21. (Sunday Telegraph - subscription required)

Dan wasan Juventus da Portugal Cristiano Ronaldo, mai shekara 35, yana son komawa Real Madrid. (Marca)

Manchester United ta shirya sayar da golanta dan kasar Argentina Sergio Romero, mai shekara 33, a watan Janairu a kan £2.5m. (Star on Sunday)

United na fuskantar yiwuwar gaza daukar dan wasan Iceland Isak Bergmann Johannesson a yayin da Juventus ta kara kaimi wajen dauko dan wasan na IFK Norrkoping mai shekara 17. (Sunday Mirror)

Kungiyar Inter Miamita David Beckhamta mayar da hankali wajen dauko dan wasanChelsea dan kasar Faransa Olivier Giroud, mai shekara 34, idan aka bude kasuwar musayar 'yan kwallo a watan Janairu. (Sunday Mirror)

Ita ma kungiyarInter Milan tana sanya ido kan Giroud, da kuma dan wasan Liverpool da Netherlands Georginio Wijnaldum, mai shekara 30. (Corriere dello Sport)

Dan wasan Sifaniya Isco ya shaida wa Real Madrid bukatarsa ta barin kungiyar, kuma kungiyar na shirin sayar da shi a kan kusan £45m, inda rahotanni ke cewa Arsenal da Manchester City na son dan wasan mai shekara 28. (Marca)

Kocin Real Madrid Zinedine Zidane ya dage cewa ba zai sayar da dan wasan Faransa Raphael Varane, mai shekara 27 ba, bayan rahotanni sun nuna cewa Manchester Unitedna son daukarsa.(Goal)

Inter Milan na son yin musayar dan wasan Denmark Christian Eriksen, mai shekara 28, da dan wasan Manchester Uniteddan kasarBrazil Fred, mai shekara 27. (Football Italia)

Kocin Inter Antonio Conte ya dage cewa tuni Eriksen ya samu "damarmaki da yawa" wajen inganta zamansa a kungiyar kuma ba zai sauya matsayi domin samar wa an wasan tsakiyar wurin zama. (Goal)