Kasuwar cinikin 'yan ƙwallon ƙafa: Makomar Grealish, Henderson, Giroud, Isco, Eriksen

Dan wasan Aston Villa Jack Grealish

Asalin hoton, Getty Images

Pep Guardiola yana son Manchester City ta dauki Jack Grealish, a yayin da ya bayyana cewa dan wasan na Aston Villa da Ingila mai shekara 25 na cikin wadanda yake son saya a yunkurinsa na inganta kungiyar, in ji jaridar Independent,

Kocin Manchester United Ole Gunnar Solskjaer ya dage cewa golansu Dean Henderson "yana so ya ci gaba da zama" a kungiyar, a yayin da ake rade radin cewa dan kwallon mai shekara 23 zai tafi zaman aro a watan Janairu. (Sky Sports)

Kocin Chelsea Frank Lampard ya ce dan wasan Faransa Olivier Giroud, mai shekara 34, wanda ke son barin kungiyar gabanin soma gasar European Championships a shekara mai zuwa, dan wasa ne "mai muhimmanci" kuma ya dage cewa yana so ya ci gaba da murza leda a Stamford Bridge. (Mirror)

Chelsea na fatan ganin Giroud ya ci gaba da zama amma ba za ta yi katsalandan ba idan dan kwallon na Faransa ya yanke shawarar tafiya. (Independent)

Real Madrid ba ta samu wani tayi ba kan dan wasan tsakiyar Sifaniya Isco, mai shekara 28, wanda ake hasashen zai tafi Manchester City ko Arsenal. (AS)

Borussia Dortmund za ta sabunta shirinta na dauko dan wasan Inter Milan dan kasar Denmark Christian Eriksen, bayan da a farkon shekarar nan aka alakanta ta da tsohon na Tottenham dan wasan mai shekara 28. (Tuttermercatoweb - in Italian)

KocinWolves Nuno Espirito Santo yana da 'kwarin gwiwa' 'yan wasansa daban-daban za su soma cin kwallaye - abin da zai rage matsin da babban mai zura musu kwallo, dan wasan Mexico Raul Jimenez, mai shekara 29 yake sha. (Express & Star)

Ole Gunnar Solskjaer ya shaida wa dan wasan Faransa Anthony Martial, mai shekara 24, cewa ba zai huta wajen murza ledar da yake yi a Manchester United ba bayan matsalar da ya fuskanta a farkon kakar wasan bana. (Mail)

QPR za ta sake yunkurin daukar dan wasan tsakiya kuma za ta bayar da aron dan wasanJamhuriyar Ireland da ke buga gasar 'yan kasa da shekara 21 Conor Masterson, mai shekara 22, idan aka bude kasuwar cinikin 'yan kwallo a watan Janairu. (West London Sport)

Kyaftin na Aston Villa Jack Grealish yana fuskantar tuhuma sakamakon zargin da ake yi masa na tukin ganganci kusa da filin wasan kungiyar a watan jiya. (Birmingham Mail)