Barcelona za ta kara da Atletico ba tare da Sergio Busquets ba

Sergio Busquets

Asalin hoton, Getty Images

Sergio Busquets ba zai buga wa Barcelona gasar La Liga da za ta yi da Atletico Madrid ba ranar Asabar, sakamakon raunin da ya yi a lokacin da ya yi wa Spaniya tamaula.

Ranar Laraba Barcelona ta sanar cewar Busquets ya yi rauni a karawar da Spaniya ta tashi 1-1 da Switzerland, amma ba ta fayyace ranar da zai koma taka leda ba.

Wasu rahotanni a Spaniya na cewar Busquets zai yi jinyar mako biyu, ba zai buga Champions League da Barca za ta ziyarci Dynamo Kiev da karawa da Osasuna a gasar La Liga a Camp Nou ba.

Dan wasa Ansu Fati na jinya shima ba zai buga wasa da Atletico ba, wadda take ta uku a teburin La Liga, bayan da Barcelona take ta takwas.

Sai dai kuma Atletico wacce Diego Simeone ke jan raga tana da 'yan kwallon da ke jinya fiye da na Barcelona.

Luis Suarez wanda ya ci kwallo biyar a La Liga ta bana, ba zai buga wasa da tsohuwar kungiyarsa ba, bayan da ya kamu da cutar korona a lokacin da yaje yi wa Uruguay tamaula.

Hector Herrera yana jinya har zuwa watan Disamba, haka kuma ba tabbas kan koshin lafiyar mai tsaron baya Stefan Savic da kuma Mario Hermoso.

'Yan wasa da suka hada da Yannick Carrasco da Diego Costa da kuma Vitolo na kokarin ganin sun koma kan ganiya kafin ranar Asabar din a wasan da zai gwada karfin Atletico a bana.