Kasuwar ‘yan kwallo: Makomar: Sancho, James, Aarons, Skriniar, Zouma

Asalin hoton, PA Media
Manchester United na ci gaba da zawarcin dan wasan Borussia Dortmund dan kasar Ingila Jadon Sancho, mai shekara 20. (ESPN)
Kazalika Manchester United za ta bar dan wasan Wales Daniel James, mai shekara 22, ya tafi Leeds United domin zaman aro, amma sai ta dauko Sancho kafin ta bar shi ya tafi. (Sun)
Bayern Munich na duba yiwuwar dauko dan wasan Norwich City mai shekara 20 dan kasar Ingila Max Aarons. (Mail)
Tottenham na son sake gwada dauko dan wasan Inter da Slovakia Milan Skriniar, sai dai ba za ta biya farashin da aka sanya kan dan wasan mai shekara 25 ba. (Guardian)
Everton da Leicester City suna son dauko dan wasan Chelsea dan kasar Faransa Kurt Zouma, mai shekara 25. (Le10 Sport, via Talksport)
Sheffield United ta mika wa Liverpool £17m don karbo dan wasan Ingila mai buga gasar 'yan kasa da shekara 21 Rhian Brewster kuma a shirye take ta hada da kudin tsarabe-tsarabe. (Sun)
Kocin Everton Carlo Ancelotti ba ya sa san dan wasan Ingila Theo Walcott, mai shekara 31, zai bar kungiyar a wannan lokacin na saye da usayar 'yan kwallo. (Mail)
Lazio tana tattaunawa don dauko dan wasan Manchester United dan kasar Brazil Andreas Pereira, mai shekara 24, domin ya yi zaman aron kakar wasa daya da kuma zabin cewa tana iya sayensa. (Telegraph)
Barcelona na dab da kammala sayen dan wasan Ajax da Amurka Sergino Dest, mai shekara 19, sai dai da wahala ta sayi karin 'yan wasa. (Goal)
Tattaunawar da Leeds United take yi ta yi nisa domin dauko dan wasan Bayern Munich Mickael Cuisance, mai shekara 21, bayan dan wasan na Faransa ya shaida wa kungiyarsa cewa yana son murza leda akai-akai. (Sport Bible, via Fabrizio Romano)
Lyon ta shirya sayar da dan wasan Faransa mai shekara 22 Houssem Aouar, wanda ake hasashen zai tafi Arsenal. (Sky Sports)











