Kasuwar ‘yan kwallo: Makomar Kante, Jorginho, Mata, King, Dias, Garcia

Manchester United ta tuntubi wakilan dan wasan Faransa N'Golo Kante domin dauko shi daga Chelsea, sai dai idan dan wasan zai tafi za a rage albashinsa na mako-mako inda ake biyansa £300,000. (Mirror)
Paris St-Germain tana tattaunawa da Chelsea domin karbo aron dan wasan Italiya Jorginho, mai shekara 28. (Telefoot, via Mail)
Lazio za ta iya soma zawarcin 'yan wasan Manchester United guda biyu - dan wasan Sufaniya mai shekara 32 Juan Mata da dan wasan Brazil Andreas Pereira, mai shekara 24. (Sun)
Tottenham na sanya ido kan dan wasan Bournemouth dan kasar Norway Joshua King, mai shekara 28 a yayin da take son dauko dan wasan gana kafin a rufe kasuwar 'yan kwallon kafa. (Telegraph - subscription required)
Kazalika Tottenham na son karbo aron dan wasan Benfica dan kasar Switzerland Haris Seferovic, mai shekara 28. (Football Insider)
Da zarar dan wasan Benfica dan kasar Portugal Ruben Dias, mai shekara 23, ya tabbatar cewa zai tafi Manchester City za ta iya sallamar dan wasan Sifaniya Eric Garcia, mai shekara 19, domin ya koma Barcelona. (Sport - in Spanish)
Aston Villa ta mika kusan £9 domin dauko dan wasan Copenhagen dan kasar Denmark Victor Nelsson, mai shekara 21. (Ekstra Bladet - in Danish)
AC Milan tana ci gaba da tattaunawa da Tottenham a kan dan wasan Ivory Coast Serge Aurier, mai shekara 27, kuma ta nemi dauko dan wasan Norwich City mai shekara 20 Max Aarons. (Mail)
Leicester City na shirin dauko dan wasan Torino mai shekara 23 dan kasar Brazil Gleison Bremer, wanda Everton ke zawarci. (Football Insider)
Barcelona ta kawo karshen zawarcin da take yi na dan wasan Inter Milan dan kasar Argentina Lautaro Martinez, mai shekara 23. (Calciomercato - in Italian)











