Liverpool 3-1 Arsenal: Mai rike da kofin Premier ta ci wasa uku a jere a bana

Asalin hoton, Getty Images
Sabon dan wasan da Liverpool ta saya a bana kan fam miliyan 45, Diogo Jota shi ne ya ci mata kwallo na uku a gasar Premier da ta yi nasara a kan Arsenal ranar Litinin a Anfield.
Arsenal wacce ta yi nasarar cin wasa biyu a jere a kakar bana ce ta fara cin kwallo a minti na 25 da take leda ta hannun Alexandre Lacazette, bayan da Andy Robertson ya yi kure.
Liverpool wacce ta ci wasa uku a jere kawo yanzu tana ta biyu a teburin Premier biye da Leicester City.
Sadio Mane ne ya ci na farko a minti na 28, bayan da golan Arsenal ya kasa tare kwallon da Mohamed Salah ya buga masa.
Liverpool,ta zura kwallo na biyu ne ta hannun Robertson tun kan a je hutu, kuma hakan ne ya kara karfin kungiyar ta Anfield a karawar.
Kungiyoyin biyu za su sake haduwa a Anfield ranar Alhamis 10 ga watan Oktoba a gasar Caraboa Cup.
Liverpool ce ta lashe kofin Premier League da aka karkare a karon farko tun bayan shekara 30.







