Coronavirus: An samu rahoton 'yan Premier 10 na dauke da cutar korona

Asalin hoton, Getty Images
An samu mutum 10 a Premier League dauke da cutar korona a wani gwaji da aka gudanar kwanan nan - gwajin da aka samu mutane da yawa dauke da annobar tun fara kakar nan.
An yi gwajin cutar korona ga jami'ai da 'yan wasa 1,595 tsakanin 21 zuwa 27 ga watan Satumba
Wadanda suka kamu da cutar da ba a bayyana sunanensu ba, za su killace kansu na kwana 10 daga nan a kara gwada su kafin su koma taka leda tare da 'yan kwallo.
Mahukuntan gasar Premier League kan gudanar da gwaje-gwajen annobar a duk mako a kungiyoyi 20 da suke buga wasannin.
Ranar 12 ga watan Satumba aka fara kakar Premier League ta bana ta 2020-21, bayan da cutar korona ta kawo tsaiko a kakar da aka kammala da ta sa aka tsayar da wasanni cikin watan Maris.
Daga baya aka ci gaba da gasar ba 'yan kallo, kuma Liverpool ce ta lashe kofin kuma karo na farko tun bayan shekara 30.







