Loris Karius: Union Berlin ta kammala daukar aron golan Liverpool

Liverpool keeper Loris Karius

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Karius ya buga wa Liverpool wasan karshe da Real Madrid ta lashe Champions League a 2018

Mai tsaron ragar Liverpool, Loris Karius ya koma buga gasar Bundesliga da zai yi wasannin aro a Union Berlin zuwa karshen kakar bana.

Mai shekara 27 dan kasar Jamus ya soke kwantiragin buga wasannin aro a Besiktas a watan Mayu, bayan da ya kusa kammala yarjejeniyar kaka biyu a Turkiya.

Karius wanda ya koma Liverpool kan fam miliyan 4.7 daga Mainz a 2016 ya buga wa Liverpool wasan karshe a karawar Champions League da Real Madrid ta lashe a 2018.

Union Berlin ta kammala gasar Bundesliga ta Jamus a bara a mataki na 11.