Loris Karius: Union Berlin ta kammala daukar aron golan Liverpool

Mai tsaron ragar Liverpool, Loris Karius ya koma buga gasar Bundesliga da zai yi wasannin aro a Union Berlin zuwa karshen kakar bana.

Mai shekara 27 dan kasar Jamus ya soke kwantiragin buga wasannin aro a Besiktas a watan Mayu, bayan da ya kusa kammala yarjejeniyar kaka biyu a Turkiya.

Karius wanda ya koma Liverpool kan fam miliyan 4.7 daga Mainz a 2016 ya buga wa Liverpool wasan karshe a karawar Champions League da Real Madrid ta lashe a 2018.

Union Berlin ta kammala gasar Bundesliga ta Jamus a bara a mataki na 11.