Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ruben Dias: Man City ta amince ta dauki dan wasan Benfica
Manchester City ta amince za ta dauki dan kwallon tawagar Portugal, mai tsaron baya, Ruben Dias daga Benfica kan fam miliyan 65.
Dan wasan City dan kasar Argentina, Nicolas Otamendi, mai shekara 32, zai koma Benfica kan fam miliyan 13.7 a wani cinikin na da ban.
Koci, Pep Guardiola ya dade yana zawarcin mai tsaron baya daga tsakiya mai amfani da hagu sosai tun bayan da Vincent Kompany ya yi ritaya a bara.
Ranar Lahadi Benfica ta fitar da wani jawabi da ya tabbatar da cinikin 'yan kwallon biyu, amma ba a kai ga rattaba hannu kan kwantiragi ba.
Dias, mai shekara 23 shi ne kyaftin din Benfica a wasan da kungiyar ta doke Moreirense ranar Asabar, ana tashi daga karawar ya dunga rungumi 'yan wasa da daraktan wasannin kungiyar Rui Costa.
Tun farko City ta yi zawarcin mai tsaron bayan Napoli, Kalidou Koulibaly, mai shekara 29 a bana, sai dai kungiyar ta Italiya ta bukaci fam miliyan 80 kudin dan wasan tawagar Senegal.