Atletico 6-1 Granada: Luis Suarez ya zura kwallo biyu a wasan farko

Luis Suarez ya ci kwallo biyu ya kuma bayar da daya aka zura a raga a wasan farko da ya fara buga wa Atletico Madrid duk da saura minti 20 aka sa shi a karawar.

Tun da fara take leda Atletico ta ci kwallo uku ta hannun Diego Costa da Angel Correa da kuma Joao Felix wanda ya koma kungiyar daga Barcelona.

Duk da Felix daga baya ya shiga karawar, amma minti biyu da shiga fili, ya bai wa Marcos Llorente kwallo shi kuma bai yi wata-wata ba ya zura a raga.

Daga nan ne Atletico ta bugo kwallo ta hannun Llorente, nan da nan Suarez ya sa kai ta fada raga sannan ya kara na shiga.

Suarez, mai shekara 33 ya kammala komawa Atletico ranar Juma'a, kuma shi ne dan Barcelona na uku kan gaba a cin kwallaye a tarihi mai 198 a raga a wasa 283 a shekara shida da ya yi a Camp Nou.

Dan wasan Ururauag ya zama na farko da ya ci wa Atletico kwallo biyu da fara wasansa, kuma na farko da ya ci kwallo ya kuma bayar aka zura a raga a karawar dan wasa ta farko a La Liga a kungiyar.