Coronavirus: An soke shirin 'yan kallo su shiga kallon wasanni

Asalin hoton, Getty Images
Firai Minista, Boris Johnson ya tabbatar da dakatar da shirin 'yan kallo su fara zuwa sitadiya a Ingila daga ranar 1 ga watan Oktoba.
Tun farko an dakatar da shirin ne bayan da ake samun karuwar masu kamuwa da cutar korona.
"Mun tabbatar da watsuwar annobar zai shafi kokarin da muke na bude wuraren kallon wasanni," in ji Firai Ministan.
A ranar Talata, Johnson ya sanar da karin matakan kariya da kasar ta dauka da ya hada da hana magoya baya zuwa kallon wasanni a sitadiya.
Ya kuma ƙara da cewar matakan kariya na hana yada cutar korona da gwamnati ta gindaya za su ci gaba da kasancewa zuwa wata shida.
Tun da fara an tsara 'yan kallo 1,000 su shiga sitadiya tare da matakan hana yada cutar korona, amma yanzu an dakatar da hakan.
An ci gaba da buga wasanni a Ingila ba tare da 'yan kallo ba, tun lokacin da annobar ta ɓulla a cikin watan Maris.
Cikin wasannin da aka aka yi ba 'yan kallon sun haɗa da Gasar Premier League da wasan karshe na FA Cup da gasar kwallon Kurket da kuma tseren Formula 1 biyu da aka yi a Siverstone.











