Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Mbappe, Alli, Suarez, Morata, Brewster, Telles, Arias

Kylian Mbappe

Asalin hoton, Getty Images

Liverpool da Real Madrid za su yi kokarin sayen dan wasan Faransa Kylian Mbappe, mai shekara 21, daga Paris St-Germain a bazara mai zuwa, a cewar jaridar L'Equipe - in French.

Real Madrid ba ta da niyyar dauko dan wasan Ingila Dele Alli, mai shekara 24, dagaTottenham. (Talksport)

Crystal Palace ta musanta rahotannin da ke cewa ta nemi dauko dan wasan Liverpool da Ingila Rhian Brewster, mai shekara 20 a kan £25m. (Goal)

Everton na tattaunawa domin dauko dan wasan Atletico Madrid da Colombia Santiago Arias, mai shekara 28. (Liverpool Echo)

Dan wasanPorto Alex Telles yana fatan kammala tafiyaManchester United sai dai har yanzu kungiyoyin biyu ba su amince da farashin sayar da dan wasan na Brazil mai shekara 27 ba. (Guardian)

Matsayin Manchester United ya sauya kan burinta na dauko Telles bayan kayen da ta sha ranar Asabar a karawarta da Crystal Palace. (Manchester Evening News)

Kazalika United tana son dauko dan wasan RB Leipzig da Faransa Dayot Upamecano, mai shekara 21. (Telegraph)

Sevilla ta tabbatar cewa ta ki amincewa da tayin sayar da dan wasanta Jules Kounde. Ana hasashen cewa dan kwallon Faransa mai shekara 21 zai tafi Manchester City. (Goal)

Tsohon dan wasan tawagar matasan Liverpool Bobby Duncan, mai shekara 19, yana shirinFiorentina domin tafiya Derby County. (The Athletic)

Dan wasan Sufaniya Alvaro Morata, mai shekara 27, yana dab da kammala komawa Juventus daga Atletico Madrid. (Goal)

Dan wasan Uruguay mai shekara 33, Luis Suarez, ya amince ya kawo karshen zamansa a Barcelona domin ya samu damar tafiya Atletico Madrid. (RMC - via Mail)

Spartak Moscow tana son dan wasan Tottenham da Ivory Coast Serge Aurier, mai shekara 27. (Sky Sports - via Boot Room)

An nemi Real Madrid ta dauki dan wasanUruguay Edinson Cavani, mai shekara 33, bayana barin Paris St-Germain. (Marca)