Kasuwar ‘yan kwallo: Makomar Alli, Rudiger, Lacazette, Brewster, Morrison, Vidal

Antonio Rudiger

Asalin hoton, Getty Images

'Yan wasan Tottenham sun cika da mamakin yadda aka ki sa Dele Alli, wanda ake rade radin zai tafi Paris St-Germain, a karawar da suka doke Southampton ranar Lahadi. (Mail)

Babu tabbas kan makomar Antonio Rudiger a Chelsea bayan da aka ki sanya shi a tawagar da ta sha kashi a hannun Liverpool ranar Lahadi, duk da cewa lafiya kalau dan wasan mai shekara 27 yake. (Mail)

Kocin Arsenal Mikel Arteta ya ce kungiyar ba ta tattaunawa da Alexandre Lacazette kan tsawaita zamansa, a yayin da kasa da shekara biyu kawai ya rage a kwangilar dan wasan mai shekara 29. (Mirror)

Fulham ta nemi dauko dan wasan Sassuolo Marlon, kuma daraktan kungiyar ta Italiya Giovanni Carnevali ya ce ana tattaunawa kan dan kwallon mai shekara 25. (Sky Sports Italia, via Football Italia)

Dan wasan Brazil Alex Telles, mai shekara 27, ya dage cewa yana mayar da hankali don murza leda a Porto, duk da rahotannin da ke alakanta shi da son tafiya Manchester United. (Sport TV, via Metro)

Dan wasan Manchester United dan kasar Ingila Luke Shaw, mai shekara 25, ya ce akwai bukatar kungiyar ta sayi karin 'yan wasa domin karfafa tawagar Old Trafford. (TV2, via Manchester Evening News)

Crystal Palace ce a kan gaba a yunkurin dauko dan wasan Liverpool mai shekara 20 Rhian Brewster, a yayin da Sheffield United da West Brom su ma suke zawarcin dan wasan na Ingila da ke murza leda a rukunin 'yan kasa da shekara 21.(Mail)

Liverpool ba ta da niyyar sayar da dan wasan Ingila mai shekara 27 Alex Oxlade-Chamberlain, wanda ake rade radin zai tafi Wolves. (Mirror)

Leicester City za ta bi sahun Tottenham a yunkurin dauko dan wasan Beijing Guoan da Koriya ta Kudu Kim Min-jae, mai shekara 23. (90min)