Guardiola ya ce ya cancanci a tsawaita zamansa a Man City

Asalin hoton, Getty Images
Pep Guardiola ya ce ya cancanci a tsawaita zamansa a Manchester City maimakon masa tayin ci gaba da jan ragamar kungiyar.
A karshen kakar bana kwantiragin kocin dan kasar Spaniya zai kare a Etihad, kuma mahukuntan kungiyar na son ci gaba da aiki da shi.
Guardiola, mai shekara 49 zai ja ragamar City kaka ta biyar daga ranar Litinin a wasa da Wolverhampton a gasar Premier League ta bana.
Hakan ya sa kocin ya dade yana horar da Manchester City fiye da zaman da ya yi a Barcelona da kuma Bayern Munich.
"Ina son na dade ina horar da kungiyar nan," kamar yadda ya fada.
"Wuri ne da nake son ci gaba da zama, amma sai idan na cancanta. Kungiyar nan ta hau kan turbar nasara, saboda haka dole mu kare martabar mu."
Sai dai kuma Guardiola ya ce kawo yanzu shugaba Khaldoon Al Mubarak ko babban jami'i Ferran Soriano babu wanda ya ce masa komai.
Zuwa yanzu Guardiola ya sayo yan wasa biyu da suka hada da Ferran Torres and Dutch centre-back Nathan Ake.
Haka kuma Fernandinho shi ne sabon kyaftin din Manchester City domin maye gurbin David Silva., bayan da 'yan wasan City suka amince ya wakilce su.











