Pep Guardiola ya ce ya kamata a bai wa Manchester City hakuri

Pep Guardiola talks to his Man City players

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Manchester City tana mataki na biyu a kan teburin Premier League na bana

Pep Guardiola ya ce ya kamata a nemi gafarar a wajensu, bayan da kungiyar ta yi nasarar daukaka kara da Uefa ta dakatar da Manchester City buga kaka biyu a Zakarun Turai.

A ranar Litinin kotun sauraren kararrakin wasanni ta duniya ta wanke City da soso da sabulu kan zargin karya ka'idar Uefa har da ta kashe kudi fiye da kima tsakanin 2012 zuwa 2016.

"Dukkan abubuwan da muka yi, mun yi sune bisa ka'ida, kuma duk masu horar da kwallon kafa sun san an yi mana illa," in ji Guardiola.

"Ya kamata a nemi gafarar mu''.

A cikin watan Fabarairu hukumar kwallon kafar Turai, Uefa ta dakatar da Man City daga shiga gasar Zakarun Turai da hukuncin ya kamata ya fara daga kakar badi.

Sai dai kuma yanzu kotun sauraren kararrakin wasanni ta duniya ta wanke City ta kuma rage tarar da aka ci kungiyar Fam miliyan 26.9 yanzu ya koma fam miliyan 9.

A gasar Champions League ta bana, City za ta karbi bakuncin Real Madrid a wasa na biyu na kungiyoyi 16 da suka rage a gasar.

City za ta karbi bakuncin Real ranar 7 ga watan Agusta a Etihad.

A wasan farko City ce ta yi nasara da ci 2-1 a karawar da suka yi a Spaniya, idan ta yi nasara za ta hadu a wasan gaba da Juventus ko kuma Lyon.