Madrid na bukatar maki biyu nan gaba ta lashe La Liga

Asalin hoton, Real Madrid Twitter
- Marubuci, Mohammed Abdu
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa
Real Madrid ta yi nasarar doke Granada da ci 2-1 a wasan mako na 36 a gasar La Liga da suka fafata ranar Litinin.
Ferland Mendy ne ya fara ci wa Real kwallo a minti na 10 da fara tamaula, kuma minti shida tsakani Karim Benzema ya kara na biyu.
Granada ta zare daya ta hannun Darwin Machis, minti biyar da suka koma zagaye na biyu na wasan.
A wasan farko da suka kara a kakar bana a Santigo Bernabeu, Real ce ta yi nasara da ci 4-2 ranar 5 ga watan Oktoban 2019.
Da wannan sakamakon Real Madrid tana mataki na daya a kan teburin La Liga da tazarar maki hudu kenan tsakaninta da Barcelona ta biyu mai rike da kofin bara.
Ita kuwa Granada mai maki 50 tana ta koma ta 10 a kan teburin wasannin shekarar nan.
Kuma saura wasa bibiyu suka rage a karkare gasar La Liga ta bana.
'Yan wasa 23 da Real Madrid ta je Granada da su:
Masu tsaron raga: Courtois da Areola da kuma Altube.
Masu tsaron baya: Carvajal da Militão da Ramos da Varane da Mendy da Javi Hernández da kuma Miguel Gutiérrez.
Masu buga tsakiya: Kroos da Modric da Casemiro da Valverde da kuma Isco.
Masu buga gaba: Hazard da Benzema da Bale da Lucas Vázquez da Asensio da Brahim da Vinicius Jr. da kuma Rodrygo.
Wasannin mako na 37 ranar Alhamis 16 ga watan Yuli:
- Athletic de Bilbaoda Leganes
- Barcelona da Osasuna
- Real Betis da Deportivo Alaves
- Celta de Vigo da Levante
- Real Mallorca da Granada
- Real Madrid da Villarreal
- Real Sociedad da Sevilla
- Valencia da Espanyol
- Getafe da Atletico de Madrid
- Eibar da Real Valladolid
Madrid ta koma mataki na daya a kan teburi, bayan da ta lashe wasa tara a jere, tun bayan da aka ci gaba da La Liga, wacce aka dakatar cikin watan Maris, saboda cutar korona.
Rabon da Real ta yi rashin nasara tun 8 ga watan Maris, inda Real Betis ta doke ta da ci 2-1 a gasar La Liga, daga nan aka dakatar da wasannin gasar ta Spaniya, saboda annobar.
Bayan da aka dauki matakan kariya daga yada annobar aka ci gaba da buga gasar La Liga, shi ne kawo yanzu Madrid ta yi nasara a karawa tara da ta fafata.
Wasanni takwas da Real Madrid ta yi nasara tun da aka ci gaba da gasar La Liga a cikin watan Yuni zuwa Yali:
- Real Madrid 3 - 1Eibar
- Real Madrid 3 - 0Valencia
- Sociedad 1 - 2 Real Madrid
- Real Madrid 2 - 0Mallorca
- Espanyol 0 - 1 Real Madrid
- Real Madrid 1 - 0Getafe
- Ath Bilbao 0 - 1 Real Madrid
- Real Madrid 2 - 0 Alaves
- Granada 1 - 2 Real Madrid
Rabon da Real Madrid ta jera cin wasa haka tun bayan shekara hudu lokacin da Zinedine ZXidane ya fara jan ragamar kungiyar.
Bayan da Real ta kori Rafa Benitez ne ta bai wa Zidane aikin horar da ita, kuma wata biyu da ya kama aiki tun daga cin da Antoine Griezman ya yi a Bernabeu daga nan ta fara jera cin wasanni.
Madrid ta kuma fara da lashe karawar da suka rage a gabanta da suka hada da Levante da Celta Vigo da Las Palmas da Sevilla da Barcelona da Eibar,
Sauran da suka bi layi da Real ta doke sun hada da Getafe da Villarreal da Rayo Vallecano da Real Sociedad da Valencia da kuma Deportivo La Coruna.
Sai da Real ta yi nasara a wasa 16 har da doke Real Sociedad da Celta da Osasuna da kuma Espanyol.
Wasa 12 daga ciki a La Liga a karshen kakar 2015/16 ta yi nasara, amma hakan bai sa ta lashe kofin ba, amma dai ita ce ta zama zakara a Champions League a kakar bayan da ta doke Atletico Madrid.
Sai a kakar 2016/17 Real Madrid ta yi nasarar cin La Liga, wanda ta karba a hannun Barcelona.
Ga jerin wadanda suka lashe La Liga da yawan kofunan da suka dauka:
- Real Madrid 33
- FC Barcelona 26
- Atletico de Madrid 10
- Athletic de Bilbao 8
- Valencia 6
- Real Sociedad 2
- Deportivo La Coruna 1
- Sevilla FC 1
- Real Betis 1











