Wolves tasha kashi a gida a hannun Manchester City

Manchester City players celebrate

Asalin hoton, Getty Images

Manchester City ta fara kakar bana ta Premier League da kafar dama, bayan da ta doke Wolves da ci 3-1 a karawar da suka yi a Molineux.

City ta fara cin kwallo ta hannun Kevin de Bruyne, sannan dan kwallon tawagar Ingila Phil Foden ya kara na biyu.

City ta yi ta kai hare-hare, amma haka suka je hutu babu wacce ta zura kwallo a raga.

Daga baya ne Raul Jimenez ya zare kwallo daya daga biyun da aka zura musu, sai dai daf da za a tashi daga wasan Gabriel Jesus ya ci wa City na uku.

Da wannan sakamakon Wolves za ta ziyarci West Ham United a karawar gaba ranar Lahadi 27 ga watan Satumba.

Ita kuwa Manchester City za ta karbi bakuncin Bournemouth a wasan zagaye na uku a Caraboa Cup ranar Alhamis 24 ga wata.

Daga nan ne ta karbi bakuncin Leicester City a wasanta na mako na biyu a gasar Premier League ranar Lahadi 27 ga watan Satumba.