Arturo Vidal: Inter ta dauki dan kwallon Barcelona

Asalin hoton, Getty Images
Dan kwallon tawagar Chile, Arturo Vidal ya koma Inter Milan daga Barcelona kan fam 900,000.
Vidal mai shekara 33, zai taka leda karkashin Antonio Conte wadanda suka lashe kofin Serie A lokacin da suka buga wa Juventus tamaula.
Inter za ta fara buga gasar Serie A ta bana karawar makon farko ranar Asabar, inda za ta karbi bakuncin Fiorentina.
Vidal ya je Barcelona a 2018, bayan da ya taka leda a Bayern Munich ya kuma buga wa Juventus tamaula kaka hudu..







