Kwallon Vidal ya sa Barca ta ci gaba da sa ran La Liga

Arturo Vidal

Asalin hoton, Getty Images

Barcelona ta rage tazarar da ke tsakaninta da Real Madrid ta daya a teburi zuwa maki daya jal, bayan da ta doke Real Valladolid 1-0 ranar Asabar.

Arturo Vidal ne ya ci wa Barcelona, bayan da ya samu kwallo daga wajen Messi, sannan ya shimfida ta a raga.

Mai masaukin baki ta samu damar farke kwallon da aka zura mata sai dai ta kasa amfana har mai tsaron ragar Barca, Marc-Andre ter Stegen ya hana a ci shi.

Real Madrid wacce ke jan ragamar teburin La Liga za ta je gidan Granda ranar Litinin a gasar ta La Liga.

Da Barcelona ba ta yi nasara a kan Valladolid ba, kuma da zarar Real ta doke Granada sai a danka mata kofin La Liga na bana.

Kocin Barcelona, Quique Setien ya yi ba za ta, bayan da bai fara karawar da Luis Suarez cikin 'yan wasan farko 11 ba, a maimakonsa ya saka matashi mai shekara 20 Riqui Puig.

Bayan da Barcelona ta fara wasan da kafar dama ta kuma mamaye karawar, daga baya da ita da Messi sai suka yi sanyi karawar ta koma ba zafi.

Duk da dai Messi bai nuna kansa da yawa a wasan ba shi ne ya bayar da kwallon da aka ci kuma na 20 da ya yi wannan bajintar a La Liga ta bana.

Tsohon dan kwallon Barcelona, Xavi ya taba yin irin wannan bajintar ta bayar da kwallo 20 aka zura a raga a kakar La Liga a 2008-09.