Chelsea na kwan gaba kwan baya a Premier League

David McGoldrick

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, David McGoldrick ya ci Arsenal a FA Cup kuma shi ne ya fara zura raga a fafatawa da Chelsea

Shelffield United ta doke Chelsea 3-0 a gasar Premier League da suka fafata a Bramall Lane ranar Asabar, amma Chelse na nan ta uku a teburi.

Tun kan hutu ne Sheffield United ta zura kwallo biyu a ragar Chelsea ta hannun David McGoldrick da kuma Oliver Mcburnie.

Saura minti 13 a tashi daga wasan banda karin lokaci Sheffield ta ci na uku ta hannun David McGoldrick.

Rabonda da Sheffield United ta doke Chelsea kwallaye da yawa tun 4-2 da ta yi a Bramall Lane ranar 8 ga watan Mayun 1993 a gasar Premier Leahue.

Chelsea wacce ta yi wasa 35 tana nan a matakinta na uku a kan teburi da tazarar maki daya da Leicester mai wasa 34 da Manchester United da tazarar maki biyu da ta buga karawa 34.

Kungiyar ta Stamford Bridge ta ci wasa biyar aka doke ta a karawa biyu tun bayan da aka ci gaba da gasar Premier League wacce aka dakatar a cikin watan Maris saboda cutar korona.

Chelsea za ta karbi bakuncin Norwich City ranar Talata, kungiyar da ta fadi daga gasar shekara nan, za ta buga Championship a badi.

Sheffield United wacce ta yi wasa 35 tana mataki na shida a kan teburin Premier na bana da makinta 54.

Ranar 16 ga watan Yuli, Sheffield United za ta ziyarci Leicester City wacce take ta hudu a teburin Premier League.