Kocin Real Madrid Zinedine Zidane ya ce bai taɓa samun matsala da Gareth Bale ba

Asalin hoton, Getty Images
Kocin Real Madrid Zinedine Zidane ya ce "ban taɓa samun matsala da Gareth Bale ba", a yayin da dan wasan na Wales yake shirin tafiya domin zaman aro a Tottenham.
Bale, mai shekara 31, wanda Real ta saya a kan £85m a 2013, ya isa filin atisayen Tottenham ranar Juma'a.
Raunukan da ya rika ji, da rashin tagomashinsa da kuma rahotannin rashin jituwa tsakaninsa da Zidane sun sa an mayar da shi saniyar-ware a Madrid.
Zidane ya ce bai yi magana da Bale ba kafin ya tafi London.
Har yanzu Tottenham ba ta bayyana daukar Bale ba kuma a yau Asabar Zidane ya ce "ba mu cimma matsaya ba".
"Lamarin na da rikitarwa. Shi Bale a kodayaushe ya fi son ya samu abin da yake so. Amma ni ban taba samun matsala da Gareth ba", in ji Zidane.
"Akwai abubuwan da ke faruwa a kodayaushe. Yana so ya samu sauyi yanzu don haka babu abin da za mu ce sai fatan alheri a gare shi. Irin wadannan abubuwa suna faruwa a kwallon kafa amma ni kodayaushe ina cewa shi dan wasa ne na musamman."
Bale ya lashe Kofin Zakarun Turai hudu, Kofin La Liga biyu, Kofin Copa del Rey daya, Kofin Uefa Super Cups uku da kuma Kofin Duniya na kungiyoyi uku a Real kuma ya ci kwallo fiye da 100.
Shi ne dan wasan Ingila mafi tsada a tarihi, kuma shi ne dan kasar Ingila da ya fi zura kwallo a gasar La Liga - inda ya ci kwallo 80 sannan ya taimaka aka ci 40 a wasanni 171 da ya buga na lig.










