''Abin dariya wai za a bayar da aron Gareth Bale''

Asalin hoton, Getty Images
Jonathan Barnett ya ce abin dariya ne idan aka yanke shawarar bayar da aron Gareth Bale ga wata kungiya daga Real Madrid.
Ana akalanta Bale, mai shekara 30, cewar zai koma tsohuwar kungiyarsa Tottenham ko kuma Manchester United daga Santiago Barnabeu.
Dan wasan tawagar Wales, wanda kwantiraginsa zai kare a karshen kakar 2022, ya ci kwallo biyu a wasa tara da ya buga a La Liga a kakar bana.
Mai kula da harkokin wasan Bale, Barnett ya ce ''Abin dariya ace daya daga fitattun dan kwallo a duniya zai je wata kungiyar domin buga mata tamaula aro.''
Ya kara da cewar ''Kawo yanzu Bale yana da sauran yarjejeniyar shekara biyu da rabi, saboda haka zai ci gaba da buga wa Real Madrid kwallo.''
''Yana jin dadin zama a Real, kuma yana fatan kara lashe manyan kyautuka a Real Madrid.''
Barnett ya yi wadan nan kalaman ne, bayan da aka dakatar da batun Bale zuwa sake komawa Tottenham a cikin watan nan na Janairu.
Ana ta jita-jitar cewar dangantaka tsakanin Bale da Zinedine ta yi tsami a tsakaninsu.
Barnett ya kara da cewar ''Abubuwa za su gyaru kamar a baya, amma abin dariya ne ya je wata kungiya buga mata wasannin aro.
Ya kuma ce ''Ba kowacce kungiya ce za ta iya daukar shi ba a yanzu haka.''











