Thiago Alcantara: Liverpool ta dauki dan wasan kan fam miliyan 20

Asalin hoton, Getty Images
Liverpool ta dauki dan wasan tsakiyar Bayern Munich Thiago Alcantara da ya sanya hannu kan kwataragin shekara hudu.
Dan wasan Sifaniyan mai shekara 29, an dauke shi ne kan fam miliyan 20, sai dai zai iya karuwa daga baya zuwa fam miliyan 25.
"Wani abin farin ciki ne. Na dade ina jiran wannan lokaci kuma yanzu ina cikin farin ciki da kasancewa ta a nan," in ji dan wasan.
Thiago zai sanya lamba shida a Anfield, kuma shi ne dan wasa na biyu da kungiyar ta dauka a wannan lokaci bayan dan kasar Girka da ta dauka Kostas Tsimikas.
Ya lashe La Liga sau biyu da Barcelona kafin daga bisani ya koma Byern a 2013, inda ya lashe Bundesliga sau bakwai da Champions daya a wata Agusta.

Asalin hoton, Getty Images
Zuwan sa Anfield zai kawo karshen hasashen cewa zakarun Premier ba za su dauki kowa ba a wannan kakar.
"Babbar nasara muka cimma ta daukar shi - ina cikin farin ciki saboda a karshe hakarmu ta cimma ruwa," in ji kocin Liverpool Jurgen Klopp.
"Na san Bayern ba sa son ya tafi. Hakan ba wata matsala ba ce saboda yana da muhimmanci a kungiyar, ya taka rawar gani a kakar da ta gabata.
"Ya shirya ne don fuskantar sabon kalubalen rayuwa kuma ya amince ya taho wajenmu."










