Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Sarr, Khedira, Sancho, Dzeko, Mendy, Ings, Raya

Ismaila Sarr

Asalin hoton, Getty Images

JaridarMail ta ruwaito cewaLiverpool ta nemi dauko Ismaila Sarr kuma ta tattauna kan halin da yake ciki da Watford, wadda ke son a biya ta £36m kafin ta saki dan wasan na Senegal mai shekara 22.

Kazalika Manchester United na son daukoSarr a matsayin zabin da ya rage mata idan ta gaza dauko dan wasan Borussia Dortmund da Ingila Jadon Sancho, in ji Independent.

Old Trafford na duba yiwuwar dauko dan wasan Inter Milan dan kasar Croatia Ivan Perisic, mai shekara 31,da dan wasan Bayern Munichdan kasar FaransaKingsley Coman, mai shekara 24, da kuma dan wasan Brazil mai shekara 30 Douglas Costa daga Juventus. (ESPN)

Manchester United tana zawarcin dan wasan Jamus Sami Khedira, mai shekara 33, idan kwangilarsa ta kare a Juventus. (Sun)

Wakilin Edouard Mendy ya yi ikirarin cewa an kulla yarjejeniya inda golan na Rennes da Senegal mai shekara 28 zai tafi Chelsea. (Stades - via Star)

Brentford ta ki amincewa da tayin kusan £10m daga Arsenal kan golan Sufaniya David Raya,mai shekara 25. (Telegraph)

Arsenal ta kulla yarjejeniya da dan wasan Lyon dan kasar Faransa Houssem Aouar, mai shekara 22. (Star)

Southampton ta shaida wa Tottenham cewa dan wasanta Danny Ings, mai shekara 28, ba na sayarwa ba ne. (Mail)

Leicester City na dab da dauko aron dan wasan Turkiyya mai shekara 23 Cengiz Under daga Roma haka kuma har yanzu Brendan Rodgers na son dan wasan Burnley James Tarkowski, 27. (Sky Sports)

West Ham ta kara kudi don dauko Tarkowski amma duk da hakan Burnley ta ki sayar mata shi. (Sky Sports)

West Brom na yunkurin sayen dan wasan Aston Villa Mbwana Samatta kafin dan wasan na Tanzania mai shekara 27 ya kammala tafiya Fenerbahce. (Sun)

Edin Dzeko na shirin tafiya Juventus daga Roma kan kwangilar shekara biyu. Tafiyar dan wasan na Bosnia and Herzegovina na nufin fatan Luis Suarez na barin Barcelona zuwa Juve zai dusashe. (Goal)