Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Alli, Walcott, Garcia, Aubameyang, Smalling, Partey, Suarez

Tottenham midfielder Dele Alli

Asalin hoton, Getty Images

Tottenham za ta iya bayar da dan wasan Ingila Dele Alli, mai shekara 24, a cinikin sake dauko dan wasan Wales Gareth Bale, mai shekara 31, daga Real Madrid. (Mail)

Everton za ta iya sayar da 'yan wasa da dama, wadanda suka hada da Theo Walcott, mai shekara 31, Alex Iwobi, mai shekara 24, da kuma Moise Kean, a yayin da kungiyar ke son rage yawan 'yan wasanta. (Mirror)

Sabuwar kwangilar shekaru uku da dan wasan Gabon Pierre-Emerick Aubameyang ya sanya wa hannu a Arsenalna nufin za a rika biyansa kusan £55m har da alawus-alawus duk shekara. (Times - subscription required)

Arsenal na ci gaba da son sayen karin 'yan wasa, inda take son dauko dan wasan Atletico Madrid dan kasar Ghana Thomas Partey, mai shekara 27, da dan wasan Lyon da Faransa Houssem Aouar, mai shekara 22. (Mirror)

Bayern Munich na shirin komawa zawarcin dan wasan Ingila Callum Hudson-Odoi, mai shekara 19, ibda take sa ran Chelsea za ta amince da bukaarta ta dakar 'yan wasanta na makarantar horas d 'yan kwallon kafa. (Mail)

Barcelona za ta iya kokarin dauko dan wasan Manchester City da Sufaniya Eric Garcia, mai shekara 19, a wannan bazarar idan ta sayar da 'yan wasan Faransa Samuel Umtiti, mai shekara 26, da Jean-Clair Todibo, mai shekara 20. (Mail)

Juventus na ci gaba da nuna kwarin gwiwa a yunkurin dauko dan wasan Barcelona dan kasar Uruguay mai shekara 33 Luis Suarez, wanda ke fafutukar ganin ya samu fasfo na kasar Italiya cikin gaggawa abin da zai ba shi damar murza leda a kungiyar. (Goal)

Chelsea na dab da kammala dauko golan Senegal Edouard Mendy, mai shekara 28. (Star)

Har yanzu Inter Milan tana son kulla yarjejeniyar dindindin da dan wasan Chelsea Emerson Palmieri, mai shekara 26, sai dai ita ma West Ham tana son karbo aron dan wasan na Italiya. (Independent)