Mujallar Forbes ta ce Lionel Messi ne ɗan ƙwallon ƙafar da ya fi samun kuɗi a 2020

Asalin hoton, Getty Images
Dan wasan Barcelona Lionel Messi ya zama na farko a jadawalin da mujallar Forbes ta fitar na 'yan wasan kwallon kafa da suka fi samun kudi a for 2020.
Forbes ta yi kiyasin cewa a shekara daya Messi ya samu $126m (£97.2m) yayin da dan wasan Juventus Cristiano Ronaldo ya zo na biyu inda ya samu $117m (£90.3m).
Neymar ne ya zo na uku yayin da abokin wasansa a Paris St-Germain Kylian Mbappe ya zo na hudu.
'Yan wasan Premier League uku - Mohamed Salah, Paul Pogba da David de Gea - na cikin 'yan wasa 10 da suka fi samun kudi, haka ma dan wasan Real Madrid da Wales Gareth Bale.
Welshman Bale ne na takwas a jerin 'yan wasan inda ya samu $29m (£22.4m) duk da cewa bai taka rawar gani ba a kakar wasa ta 2019-20, abin da ya suke zaman tsama da kocin Real Zinedine Zidane kuma sau biyu kawai ya sa shi a wasa cikin wasanni 14 da ya jagoranta a kakar wasan.
Dan wasan Liverpool Salah shi ne na biyar inda yake gaban dan wasan Manchester United Pogba, wanda shi ne na shi ne na shida, yayin da golan United De Gea yake a matsayi na 10.
Dan wasan gaba na Barcelona Antoine Griezmann shi ne na bakwai yayin da dan wasan Bayern Munich Robert Lewandowski ya zo na tara.
Jerin 'yan wasan da Forbes ta ce sun fi samun kudi a 2020
- Lionel Messi (Barcelona da Argentina) $126m (£97.2m)
- Cristiano Ronaldo (Juventus da Portugal) $117m (£90.3m)
- Neymar (Paris St-Germain da Brazil) $96m (£74.1m)
- Kylian Mbappe (Paris St-Germain da Faransa) $42m (£32.4m)
- Mohamed Salah (Liverpool da Masar) $37m (£28.5m)
- Paul Pogba (Manchester United da Faransa) $34m (£26.2m)
- Antoine Griezmann (Barcelona and France) $33m (£25.5m)
- Gareth Bale (Real Madrid da Wales) $29m (£22.4m)
- Robert Lewandowski (Bayern Munich da Poland) $28m (£21.6m)
- David de Gea (Manchester United da Sufaniya) £27m (£20.8m)










