Hotunan Lionel Messi yana atisaye a Barcelona

Lionel Messi

Asalin hoton, @FcBarcelona

Lionel Messi ya fito atisaye a Barcelona a karon farko bayan ya gagara barin kulob ɗin.

Kaftin ɗin na Barcelona ya yi atisaye tare da tawagar ƙungiyar saɓanin ranar Litinin da gwarzon ɗan wasan na duniya ya yi atisaye shi kaɗai kafin samun sakamakon gwajin korona.

Messi ya yi atisaye tare da ƴan wasan Barcelona da suka haɗa da Philippe Coutinho da Sergio Busquets da Frenkie de Jong da Ansu Fati.

Messi na shirin tunkarar wata kakar wasa a Barcelona, bayan hana shi barin ƙungiyar da shugabanta ya ce an biya kudin darajarsa yuro miliyan 700 kafin ta bari ya tafi.

Bayan sanar da cewa zai ci gaba da taka leda a Barcelona, Messi ya ce yana fatan za a samu sauyi a Barcelona musamman sabon koci da aka ɗauka.

Sai dai Messi mai shekara 33 ya ce za su zura ido su ga ko sauyin zai yi wani tasiri a manyan wasanni.

Messi wanda ya lashe kyautar gwarzon ɗan wasan kwallon ƙafa na duniya sau shida - ya bayyana damuwarsa game da abokansa biyu Luis Suarez da Arturo Vidal da ake tunanin za su koma taka leda a gasar Seria A a Juventus da Inter Milan.

Kashin da Barcelona ta sha ci 8-2 hannun Bayern Munich a gasar zakarun Turai shi ya harzuƙa Messi har ya sanar da yanke ƙauna da ƙungiyar da ya shafe ƙuriciyarsa.

Wulaƙancin da Bayern ta yi wa Barcelona ne ya sa ta kori Quique Setien ta ɗauko Koeman

Ga yadda Messi ya yi atisaye a Barcelona

Lionel Messi

Asalin hoton, @FCBarcelona

Lionel Messi

Asalin hoton, @FCBarcelona

Lionel Messi

Asalin hoton, @FCBarcelona

Lionel Messi

Asalin hoton, @FCBarcelona

Lionel Messi

Asalin hoton, @FCBarcelona