Barcelona: Me zai faru bayan wulaƙancin 8-2 a hannun Bayern Munich?

Asalin hoton, EPA
Kashin da Barcelona ta sha a hannun Bayern Munich ya kasance dare mafi wulakanci yayin da ta fice daga gasar Zakarun Turai ta Champions League.
Masharhanta ƙwallon ƙafa sun kira ci 8-2 da aka yi wa Barcelona a matsayin "abin kunya", yayin da mai sharhi kan ƙwallon ƙafa Guillem ya ce "an watsar da martabar Barcelona a shara."
Ɗan wasan baya da ya shafe lokaci yana taka leda, Gerard Pique ya kasa danne haƙurinsa inda ya ce dole akwai buƙatar sauyi - yayin da ake ta yaɗa rahotanni cewa za a kori kocin Barcelona Quique Setien, wanda aka naɗa a watan Janairu.
Yanzu me zai biyo baya ga Barcelona, ƙungiyar da ta lashe kofin na Champions League sau biyar kuma ɗaya daga cikin manyan ƙungiyoyin da a baya ake tsoro?
'Ba duka ne laifin Setien ba'
Bayan kasancewa ta biyu a La Liga bayan Real Madrid, tuni Setien ke fuskantar matsin lamba wanda duka wata bakwai da ɗaukarsa kan yarjejeniyar shekara biyu da rabi.
Damarsa ta ci gaba da aikinsa bayan wulaƙancin da aka yi wa Barcelona a Lisbon kaɗan ce, yayin da tuni ake yaɗa rahotannin cewa har Barca ta yanke hukuncin sallamarsa.
"Za a kore shi, ba zai daɗe ba," in ji Chris Sutton a kafar BBC Radio 5, wanda ya lashe kofin Premier League da Blackbun Rovers.
Ba za a iya wulaƙanta mutum kamar haka ba a matsayin manajan Barcelona. kuma wannan shi ne - wulaƙanci ne."

Asalin hoton, Reuters
Balague ya ce ba daidai ba ne a ɗora dukkanin laifin shsan kashin a kan Setien, yana mai cewa abin da ya faru Juma'a koma-bayan da Barcelona ke fuskanta ne a tsawon shekaru.
"Shi ne zaɓi na huɗu lokacin da aka naɗa shi," kamar yadda Balague ya shaida wa BBC Radio 5.
"Wannan ne wasansa na uku baki ɗaya a gasar Zakarun Turai. Amma ba zai zama laifin zaɓensa ba kuma ba laifinsa ba ne kan abin da ke faruwa.
Babu wanda zai iya gane abin da ke faruwa. Siyasa ce ta mamaye Barcelona kuma 'ƴan wasa ke gudanar da ita.
Mai sharhi kan ƙwallon ƙafa a Spain Andy West ya ce Setien "yana sane cewa za a kore shi".
"Setien babu wata abota da ya ƙulla a tsakanin ƴan wasa tun naɗa shi a Janairu tsakaninsa da manyan ƴan wasa da suka ƙunshi Messi - ba su damu da bin tsarinsa ba da yake so," a cewarsa.
Wa zai gaji Setien?
Tsohon kocin Tottenham Mauricio Pochettino da kuma tsohon kocin Everton Ronald Koeman, ana alaƙanta su da Barcelona.
Koeman, wanda ke horar da Netherlands tun 2018, ya shafe shekara shida yana taka leda a Barcelona tsakanin 1989 zuwa 1995, yayin da Pochettino bai samu aiki ba tun lokacin da Tottenham ta raba gari da shi a watan Nuwamban 2019.
"Pochettino na nan kuma wani mutum ne wanda ya fahimci ƙungiyar," inji Balague.
"Shugaban Barcelona Josep Maria Bartomeu da Pochettino abokanai ne."
'Wani abin da ke faruwa a Barca'
Sutton, wanda ya kalli yadda aka wulaƙanta Barcelona ya ce ƙungiyar tana ƙunshe ne da ƴan wasan da shekarunsu suka ja.
Ya ce Sergio Busquets, mai shekara 32, wanda ya lashe La liga sau takwas ba shi da ƙafafun taka leda a yanzu domin riƙe tsakiya, yayin da kuma tsohon ɗan wasan Liverpool Luis Suarez ya sauya daga ɗan wasan da aka san shi.
Sutton ya ƙara da cewa: "Ba zan taɓa tuna lokacin da aka yi wa Barcelona irin wannan walaƙanci ba."

Asalin hoton, EPA
"Wannan abin kunya ne. Tsoffin ƴan wasa ne suka cika Barcelona."
'Ruɓewa'
Barcelona ba ta lashe kofin Champions League ba tun kakar 2014-15.
West ya ce Bartomeu bai ɗauki mataki ba ga taɓarɓarewar kulob ɗin.
"Abu mafi muni ma shi ne yadda kulob ɗin ke fuskantar matsalar kuɗi wanda zai ƙara haifar da ƙalubalen farfaɗo da ƙungiyar," a cewarsa.
"Yanzu Barcelona ta fi son ta sayar da yan wasa maimakon ta saya, musamman manyan ƴan wasanta da suka ƙunshi Ivan Rakitic da Arturo Vidal, wataƙila ma har da Suarez da ake tunanin za su tafi nan da makwanni.
"Kulub ɗin ya ruɓe matuƙa, kuma ya fara tun daga sama."
Yadda abubuwa suka taɓarɓare wa Barcelona
- Wannan shi ne kashi mafi muni da Barcelona ta sha wanda ya zarta ci 6-2 bayan wanda da ta sha a hannun Valencia a Satumban 1962
- Karo na farko da aka ci Barca ƙwallaye takwas kenan tun 8-0 da Sevilla ta ci ta a Afrilun 1946
- Wannan shi ne karon farko da aka ci Barcelona da tazarar ƙwallo shida tun Afrilun 1951, inda Espanyol ta doke ta 6-0 a LaLiga
- Waɗannan ne ƙwallaye huɗu mafi sauri da aka ci a gasar Zakarun Turai tun da Bayern ta zira ƙwallo huɗu a ragar Porto cikin minti 36 a kakar 2014-15
- Wannan ce kakar farko da Barcelona ta ƙare ba kofi tun kakar 2013-14











