Jurgen Klopp: Kocin Liverpool aka zaɓa gwarzon kocin Premier League a bana

Asalin hoton, Getty Images
Kocin Liverpool Jurgen Klopp aka zaɓa gwarzon kocin gasar Premier League a bana.
Kocin na Jamus mai shekara 53 shi ya taimaka wa Liverpool lashe kofin gasar karon farko cikin shekaru 30.
Liverpool ta haɗa maki 99, inda ta lashe wasa 32 a wasanni 38, tazarar maki 18 tsakaninta da Manchester City.
Klopp ya doke kocin Chelsea Frank Lampard, da na Leicester Brendan Rodgers da kuma na Sheffield United Chris Wilder a takarar gwarzon kocin.
A watan da ya gabata shi ne aka zaɓa gwarzon kocin shekara na ƙungiyar koca-kocai.
Ɗan wasan baya na Liverpool Trent Alexander-Arnold, mai shekara 21, shi ya lashe kyautar gwarzon matashin ɗan wasa a bikin da aka gudanar ranar Juma'a.
Masoya ƙwallon ƙafa ne suka zaɓi gwarzayen daga ƙuri'unsu da aka tattara haɗi da na masana ƙwallon ƙafa






