Willian ya tafi Arsenal daga Chelsea

Asalin hoton, Getty Images
Arsenal ta karɓo dan wasan tsakiya na Brazil Willian daga Chelsea bayan kwangiyarsa ta kawo ƙarshe.
Chelsea ta yi wa ɗan wasan tayin sabuwar kwangila amma bai kai tsokar kwangilar da Arsenal ta ba ɗan wasan mai shekara 32 ba.
"Na yarda shi dan wasa ne da zai kawo sauyi," a cewar kocin Arsenal Mikel Arteta.
"Muna da niyar mu gyara gabanmu musamman da wasan da zai iya riƙe tsakiya kuma ya kutsa gaba."
Willian ya buga wa Chelsea wasa 339 bayan ta ɗauko shi daga kungiyar Anzhi Makachkala ta Rasha kan miliyan £30 a shekarar 2013.
Ya lashe kofuna manya biyar a Chelsea, a ciki akwai gasar Premier league biyu da Europa league daya, kuma ya ci lambar yabo ta gwarzon dan kwallon kafar shekara.
"Shi dan wasa ne da yake iya buga wasa a bangarori daban-daban - zai iya buga wurare uku ko hudu," in ji Arteta.
"Yana da kwarewa a kan komai a duniyar kwallon kafa amma har yanzu yana da burin zuwa nan ya murza mana yadda ya kamata."
"Nayi sha'awar maganganun da nayi da shi da yanda ya matsu ya zo"
Arsenal ta gama kakar gasar Premier League da ta wuce a mataki na takwas, yayin da Chelsea kuma ta gama ta mataki na hudu kuma ta samu gurbin gasar Zakarun Turai.











