Kasuwar 'yan ƙwallo: Makomar Willian, Dembele, Sancho, Grealish, Chilwell, Sanchez

Asalin hoton, Reuters
Dan wasan Chelsea Willian, mai shekara 31, ya ki sanya hannu kan kwangilar karin shekara biyu a kungiyar kuma ya tattauna da Arsenal, wacce ta amince ta ba dan wasan na Brazil kwangilar shekara uku kamar yadda ya so. (Guardian)
Kazalika Arsenal na son dauko dan wasanBayern Munich dan kasar Brazil Philippe Coutinho, mai shekara 28, da kuma dan wasan Atletico Madrid dan kasar Ghana Thomas Partey, mai shekara 27. (Times - subscription required)
Dan wasanArsenal Pierre-Emerick Aubameyang yana so kungiyar ta sayo dan wasan Barcelona dan kasar Faransa Ousmane Dembele, mai shekara 23. (Le10 Sport)
Manchester United na dab da dauko dan wasanBorussia Dortmund da Ingila mai shekara 20 Jadon Sancho inda zai sanya hannu kan akalla kwangilar shekara biyar. (Mail)
Manchester United za ta jira har sai an kusa rufe kasuwar musayar 'yan kwallo domin tana son dauko dan wasan Aston Villa da Ingila Jack Grealish, mai shekara 24. (Mail)
Inter Milan ta amince ta sayi dan wasan Chile Alexis Sanchez, mai shekara 31, a kan £13.5m daga Manchester United kuma za a sanar da hakan ne bayan wasan da kungiyar za ta fafata da Getafe ranar Laraba. (Corriere della Sera, via Mail)
Kocin Chelsea Frank Lampard zai sayar da 'yan wasan da ke tsaron baya biyar kuma zai soma tsara yadda zai sayi dan wasan Leicester City da Ingila Ben Chilwell, mai shekara 23. (Times - subscription required)
Haka kumaChelsea tana sha'awar dauko dan wasan Real Madrid dan kasar Sufaniya mai shekara 23 Sergio Reguilon, wanda Everton ta taya a kan £18m.(Sky Sports)
Paris St-Germain tana son sayar da tsohon dan wasan Everton Idrissa Gueye kuma Wolves tana sha'awar sayen dan wasan na Senegal. (Le10 Sport)
AC Milan za ta fuskanci kalubale daga Bayer Leverkusen wajen dauko dan wasan Norwich City Ben Godfrey, mai shekara 22, wanda za a sayar a kan £30m. (Sky Sports)
Lazio, Tottenham, RB Leipzig, Everton da kuma PSV Eindhoven suna son dauko dan wasan Koriya ta Kudu Kim Min-jae, dan shekara 23. (Gazzetta dello Sport)
Borussia Dortmund na dab da sayen dan wasan Manchester City1 dan shekara 15 Jamie Bynoe-Gittens. (Mail)











