FA CUP: Arsenal ta kai Europa da kyar da gumin goshi

Asalin hoton, Getty Images
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal ta lashe gasar kofin kalubale ta ƙasar Ingila wato FA Cup bayan ta doke abokiyar hamayyarta Chealsea da ci biyu da daya.
Da farko dai Chelsea ce ke kan gaba a wasan amma sai labari ya sauya daga bisani inda Arsenal ta farfaɗo ta farke kwallon da Chelsea ta zura mata a raga ta hannun Pierre Emerick Aubameyang.
A zagaye na biyu ma ɗan wasan ya kara zura kwallo ta biyu.
Yayin da ake wasan Chelsea ta rasa ɗan wasanta na tsakiya Mateo Kovacik bayan da alƙalin wasa ya nuna masa jan kati.
An dai yi wasan ne ba tare da 'yan kallo da yawa ba saboda annobar korona.







