Arsenal na son Carlos, Manchester United na zawarcin Gabriel Magalhaes

Diego Carlos

Asalin hoton, Getty Images

Arsenal na son dauko dan wasan Sevillamai shekara 27 dan kasar Brazil Diego Carlos a yayin da koci Mikel Arteta ke shirin yi wa kungiyar garambawul a bazara. (Telegraph - subscription required)

A cikin wannan makon Arsenal za ta yi tayin bai wa dan wasan Gabon Pierre-Emerick Aubameyang, mai shekara 31, £250,000 duk mako a yunkurinta rarrashinsa ya zauna a kungiyar. (Mirror)

Sai dai Aubameyang yana so Arsenal ta sayo manyan 'yan wasa kafin ya amince ya sabunta kwangilarsa bayan ya taimaka wa kungiyar wajen lashe Kofin FA karo na 14. (Le10 Sport, via Metro)

An yi wa kocin Tottenham Jose Mourinho tayin dauko dan wasan Watford dan kasar IngilaTroy Deeney, mai shekara 32, domin maye gurbin Harry Kane. (Mail)

Aston Villa na son dauko dan wasan Liverpool mai shekara 25 dan kasar Belgium Divock Origi a bazara. (Sun)

Liverpool ta sha gabanParis St-Germain a fafatawar da suke yi ta dauko dan wasan Bayern Munich Thiago Alcantara kuma yanzu 'akwai yiwuwar' ta sayo dan wasan na Sufaniya. (Mundo Deportivo, via talkSPORT)

ShugabanManchester United Ed Woodward ya tattauna da wakilan dan wasan Lille Gabriel Magalhaes domin yiwuwar dauko dan wasan na kasar Brazil mai shekara 22. (RMC Sport, via Express)

A bangare guda, United na fatan sanya Chris Smalling, mai shekara 30, a cikin yarjejeniyar da za ta kai ga dauko dan wasan Inter Milan mai shekara 25 dan kasar Slovakia Milan Skriniar - sai dai Roma tana ci gaba da yunkurin kulla yarjejeniya da dan wasa na Ingila bayan ya taka rawar gani a yayin da yake zaman aro a kungiyar ta kasar Italiya. (Star)

AC Milan da Napoli suna tattaunawa da dan wasan Norwich City Ben Godfrey, mai shekara 22, bayan an jefar da City daga Gasar Firimiya. (Calciomercato, via Mail)

Cardiff City tana kan gaba a yunkurin dauko dan wasan Barnsley da Wales mai shekara 27 Kieffer Moore. (WalesOnline)