Chelsea na son ɗauko Pope, dole Inter ta biya £15m idan tana son Sanchez

Asalin hoton, Reuters
Chelsea ta kara kaimi a yunkurinta na dauko golan Burnley dan kasar Ingila Nick Pope, mai shekara 28, a yayin da makomar golan sufaniya Kepa Arrizabalaga, mai shekara 25, take kasa-tana-dabo. (Star Sunday)
Crystal Palace tana zawarcin dan wasan Watford dan kasar Senegal Ismaila Sarr, dan shekara 22, kuma za ta iya yin tayin £40m kan dan wasan Ivory Coast Wilfried Zaha, mai shekara 27, wanda akesa ran zai bar Selhurst Park. (Sun on Sunday)
Manchester United ta bukaci Inter Milan ta biya £15m domin sayen dan wasan Chile Alexis Sanchez, mai shekara 31, gaba daya. (Sunday Express)
Daraktan wasanni naAC Milan Paolo Maldini ya ce yana kallon tsohon dan wasan Sweden Zlatan Ibrahimovic, mai shekara 38, matsayin mutumin da zai buga tamaula tare da su a kakar wasa mai zuwa. (ESPN)
Paris St-Germain tana shirin taya dan wasan Sufaniya Thiago Alcantara kuma a sirye take ta biya farashin da Bayern Munichta sanya a kan dan wasan mai shekara 29 wanda Liverpool take zawarci. (Le10Sport)
Manchester City na son dauko dan wasan Barcelona Sergi Roberto, mai shekara 28, a yayin da dan wasan City mai shekara 19-year Eric Garcia yake shirin tafiya Barca. (Sport)
Everton tana son gwada sa'arta inda ta ware £15m don karbo dan wasan Bournemouth dan kasar Norway Joshua King, mai shekara 28. (Sun on Sunday)
A gefe guda, har yanzuEverton ba ta taya dan wasanReal Madrid Sergio Reguilon ba duk a rahotannin da ke cewa tun da farko ta mika £18m don karbo dan wasan na Sufaniya mai shekara 23. (Liverpool Echo)
Juventus tana duba yiwuwar mka dan wasan Italiya mai shekara 26 Federico Bernardeschi ga Manchester United a wani bangare na yarjejeniyar dauko dan wasan Ingila Chris Smalling, mai shekara 30, a bazarar nan. (Inside Futbol)
KazalikaJuve na son dauo dan wasan Roma dan shekara 21 dan kasar Italiya Nicolo Zaniolo. (Tuttosport)
Bournemouth za ta yi bakin kokarinta wajen ganin dan wasan Wales mai shekara 23 David Brooks ya zauna a kungiyar, a yayin da Tottenham, Everton da kuma West Ham suke zawarcinsa. (Star Sunday)
Newcastle na shirin dauko dan wasan Sassuolo dan kasar Brazil Rogerio, mai shekara 22. (Sky Italia)
Leeds na sha'awar dauko dan wasan Gent Milad Mohammadi - a yayin da ake sa ran sayar da dan wasan na Iran mai shekara 26 kan £6.3m. (Football Insider)
Dan wasan Real Madrid dan kasar Sufaniya Borja Mayoral, mai shekara 23, wanda yake zaman aro a Levante, ya kusa tafiya Lazio. (Marca)










