Yadda Bayern ta ga bayan Barcelona

Asalin hoton, Getty Images
A ci gaba da Gasar Zakarun Turai, kungiyar Bayern Munich ta Jamus ta ragargaji Barcelona ta Spaniya da ci 8 - 2.
Karon farko ke nan da aka taba wa Barcelona irin wannan ragargazar a tarihin wasannin da ta taba bugawa a Gasar Zakarun Turai.
Wasan na cikin jerin wasannin kusa da na karshe.
A ranar Laraba, Paris St. Germain ta doke Atalanta da kwallo 2 - 1.
Ranar Alhamis ita ma kungiyar Red Bull Leipzig ta doke Atletico Madrid da ci 2 - 1.
A yanzu wasa daya ya rage - wanda za a buga a daren Asabar - tsakanin Manchester City da Lyon.
'Yan wasan kungiyar wadanda sune zakarun gasar lig ta Jamus sun rika wasan kura da 'yan Barcelona, kuma sun nuna mu su cewa su ba tsaran su ne ba.
Bayern ta jefa kwallo hudu kafin a tafi hutun rabin lokaci, sannan ta sake zura wasu hudun bayan an dawo, kuma da sun kara kaimi, to lallai da sun kara cin wasu kwallayen domin Barcelona ta dauke wuta har ta kai ga kamar suna raka 'yan wasan Bayern ne a cikin filin wasan.
Sai dai su ma 'yan wasan Bayern ma sun gaza, domin 'yan wasan gaba na Barca - wato Lionel Messi da Luiz Suarez - sun rika kai farmaki cikin gidan Bayern har sun rika auna gola Manuel Neuer.

Asalin hoton, Getty Images
Yadda abin al'ajabin ya wakana
A cikin mintuna goma na farkon wasan ne Thomas Muller ya bude shafin farko na tarihin da Bayern ta kafa bayan ya aika da kwallo ta farko cikin ragar Barcelona, sai dai Barcelona ta farke bayan da David Alaba ya kasa fitar da wata kwallon da Jordi Alba ya aika cikin 18 din Bayern.
Sai dai minti 22 da suka biyo bayan wadannan sun nuna raunin da Barca ke da shi, inda Ivan Perisic ya narka kwallon Bayern ta biyu cikin raga, kafin Serge Gnabry ya ci tasa kwallon, shi kuma Muller ya zura kwallonsa ta biyu.
Robert Lewandowski kuwa ya jefa kwallonsa ta 14 cikin wasa takwas da ya buga a gasar Zakarun Turai ta bana, shi kuma Philippe Coutinho - wanda Barcelona ta ba Bayern aron sa - ya ci kwallon Bayern ta bakwai da ta takwas.
Yanzu dai Bayern na jiran wasan Manchester City da Lyon ta Faransa da za buga cikin daren Asabar domin sanin ƙungiyar da za su kara da ita a wasan dab da na ƙarshe.

Asalin hoton, Getty Images











