Barcelona da Bayern Munich: Shin Messi zai haskaka ko Lewandowski zai danne shi?

Barcelona celebrate goal

Asalin hoton, Getty Images

Babban wasa ne tsakanin manyan kungiyoyi biyu a wasan zagayen gab da na kusa da karshe a gasar kwallon kafar Turai.

Wasa ne da zaratan 'yan wasa za su nuna kwarewarsu a gasar zakarun Turai a ranar Juma'a da yammaci.

Da dama na kallon wasan a matsayin wanda zai fayyace kungiyar da za ta lashe gasar zakarun Turai ta bana.

Messi wanda ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon duniya har sau shida zai fito gaba da gaba tare da Lewandowski na Bayern Munich wanda a kakar wasa ta bana- shi ne kan gaba wajen zura kwallaye a nahiyar Turai.

Barcelona ta yi rashin nasara a La Liga inda Real Madrid ta lashe kofin bayan ta samu nasara a wasanni biyar cikin tara kacal.

A yayin da ita kuma Bayern Munich ta lashe wasanni 19 a jere sannan kuma ta lashe gasar Bundesliga da kuma na German Cup.

Shin Barca za ta kai bantenta?

A zihiri Barcelona na kwan gaba kwan baya a kakar bana kuma tun bayan da aka koma murza leda a watan Yuni bayan hutun Korona, kungiyar ta Nou Camp ba ta haskaka ba yadda ake tunani.

Arturo Vidal and Lionel Messi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Arturo Vidal ya lashe kofuna tare da Bayern da kuma Barca

Tsohon dan kwallon Bayern Munich wanda ke murza leda a Barcelona a yanzu, Arturo Vidal ya ce su ne kan gaba a duniya kuma za su samu galaba a wasan.

"Muna da Leo Messi da kuma manyan 'yan kwallo saboda haka ba ma tsoron komai," in ji Vidal.

Shin Bayern za ta haskaka kamar a Jamus?

Yan wasan Bayern Munich

Asalin hoton, @FCBayernEN

Bayanan hoto, Barcelona ta fi shan kashi hannun Bayern Munich a Champion League

Bayern Munich ta nuna fin karfi a gasar kwallon Jamus amma hakan ba tabbas ba ne za ta nuna kwanji a gasar zakarun Turai.

Robert Lewandowski shi ne ake kallon a matsayin dan kwallon da zai iya lashe kyautar gwarzon dan kwallon duniya saboda kwallayen da ya ci a kakar bana.

Dan wasan ya ci kwallo 13 a wasa bakwai a gasar bana ta Turai kuma hakan ya nuna cewa idan har kwallon ta karbe shi a yau, tabbas 'yan wasa masu tsaron baya na Barcelona za su sha wuya.

Duk kungiyar da ta samu nasara a wannan wasan za ta hadu da Manchester City a zagayen kusa da karshe.