Champions league: Shin ko Lewandowski zai iya karya tarihin Ronaldo

Asalin hoton, Reuters
Wannan dai wata kaka ce da Robert Lewandowski ke haskakawa cikinta, ya zuwa yanzu kuma ya ci kwallaye da dama.
Sai dai dan wasan ya dage kan cewa shi ba burinsa ya kamo tarihin da Cristiano Ronaldo ya kafa ba, bayan nasarar da kungiyarsa Bayern Munich ta samu na tsallakawa zagayen daf da kusa da na karshe a gasar zakarun Turai.
Dan wasan kasar Poland din mai shekara 31 ya zira kwallo biyu a lokacin da Munich ta yi raga-raga da Chelsea a ranar Asabar da ci 4-1 wanda jumullar kwallayen sun zama 7-1.
Lewandowski ya ci kwallo 13 a wasa bakwai da ya buga na gasar Champions a wannan kakar, kuma kwallaye hudu ne tsakaninsa da tarihin da Ronaldo ya kafa na cin kwallo 17 a kaka daya a gasar, a 2013-2014 lokacin yana Real Madrid.
Idan Bayern Munich ta je wasan karshe da za a buga a Lisbon, dan wasan zai buga wasanni biyar kenan har na karshe wanda karin dama ce wajen haye tarihin Ronaldo.
"Ba kwallo na ba ce" In ji dan wasan lokacin da aka tambaye shi game da tarihin Ronaldo.
"Muna da sauran wasannin da za mu buga a wannan zagayen na siri daya kwale, kawai ina farin ciki kan yadda muke samun dama kuma muna cin kwallo."
Lewandowski zai iya kusantar tarihin koma ya haura shi, to amma yana da sauran aiki a gabansa na kamo dan wasan gaban Juventus din kafin ma ya haura shi.
Dan wasan Portugal din shi ne ya fi ko wane dan wasa cin kwallo a gasar zakarun Turai, in da yake da kwallo 130 - kwallo 64 kenan tsakanin shi da Lewandowski, wanda ya koma na hudu cikin jerin wadanda suka fi cin kwallo a gasar bayan kwallayen da ya ci Chelsea.











