Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Dembele, Silva, Watkins, Bale, Iheanacho, Thiago

Ousmane Dembele

Asalin hoton, Getty Images

Manchester United na son dauko dan wasan Barcelona mai shekara 23 dan kasar Faransa, Ousmane Dembele, a matsayin wanda zai maye gurbin dan wasan Borussia DortmundJadon Sancho, mai shekara 20, wanda har yanzu ba ta kai ga kammala yarjejeniyar dauko shi ba. (ESPN)

Watakila sai Sancho ya dauki matakin tilasta wa kungiyarsa ta bar shi ya tafi Manchester United.(Mirror)

Dan wasanManchester City dan kasar Sufaniya David Silva, mai shekara 34, zai tafi Lazio idan kwangilarsa ta kare a karshen kakar wasan bana. (Guardian)

Aston Villa tana shirin zawarcin dan wasan Brentford Ollie Watkins, mai shekara 24. (Sky Sports)

Gareth Bale ba zai bar Real Madrid a bazarar nan ba kuma dan wasan na Wales mai shekara 31 ya shirya ci gaba da zama zuwa shekara biyu har sai ya samu sabuwar kungiyar da za ta dauke shi. (Mirror)

Arsenal ta ware £25m don dauko dan wasan Ajax da Netherlands Quincy Promes, mai shekara 28. (Sun)

West Bromwich Albion, Leeds da kumaFulham suna son dauko Ryan Fraser, mai shekara 26, wanda ya bar Bournemouth a karshen watan Yuni. (90Min)

Chelsea ta matsu ta sayar wa AC Milan dan wasan Faransa mai shekara 25 Tiemoue Bakayoko kuma a shirye take ta rage farashinsa. (Sun)

Real Madrid na son ci gaba da rike dan wasanta mai shekara 24 Dani Ceballos bayan ya komo daga zaman aro aArsenal. (AS)

Leicester City ta nuna sha'awar dauko dan wasan Burnley mai shekara 24 Dwight McNeil. (Sky Sports - via Leicester Mercury)

Fenerbahce na son karbo aron dan wasan Leicester da Najeriya Kelechi Iheanacho, mai shekara 23. (Fotospor - via Sport Witness)

Dan wasanLazio Ciro Immobile ya yi ikirarin cewaNewcastle ta tuntubi wakilinsa domin yiwuwar karbo aronsa a bazarar sai dai dan wasan mai shekara 30 dan kasar Italiya ya sha alwashin ci gaba da zama a kungiyar ta Serie A. (Goal)

Sheffield United, Crystal Palace, Everton, Newcastle da kuma Southampton suna son dauko dan wasan Rangers Glen Kamara. Kazalika Dynamo Kiev da Dynamo Moscow suna sha'awar dan wasan na Finland mai shekara 24. (90Min)