Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Thiago, Sancho, Chilwell, Oblak, Willian, Partey, Dybala, Havertz

Asalin hoton, Getty Images
Liverpool ta tuntubi Bayern Munich domin yiwuwar dauko dan wasan Sufaniya Thiago Alcantara, mai shekara 29. (Bild, in German - subscription required).
Sai dai kuma, Liverpool ba ta son dauko dan wasan Vasco da Gama dan kasar Brazil Talles Magno, duk da rahotannin da ke cewa dan wasan mai shekara 18 zai tafi Anfield. (Standard)
Shugaban fannin kwallon kafa na Borussia Dortmund, Sebastian Kehl, ya jaddada cewa dan wasan Ingila mai shekara 20 Jadon Sancho zai ci gaba da zama a kungiyar duk da sha'awar da Manchester United ke yi na dauko shi. (MEN)
United na shirin fafatawa da Chelsea a yunkurin dauko dan wasan Leicester City dan kasar Ingila Ben Chilwell, mai shekara 23, a yayin da Chelsea ta ce ba za ta iya biyan £80m kan dan wasan ba. (Mirror)
Golan Atletico Madrid dan kasar Slovenia mai shekara 27 Jan Oblak zai yanke shawara kan makomarsa a yayin da aka ce Chelsea na zawarcinsa. (AS)
A karshen makon nan Arsenal za ta sanar da dauko dan wasan Brazil Willian, mai shekara 32, kan kwangilar shekara uku bayan zamansa ya kare a Chelsea. (Telegraph - subscription required)
Arsenal za ta fuskanci kalubale daga Juventus a kokarinta na dauko dan wasan Atletico Madrid mai shekara 27 dan kasar Ghana Thomas Partey. (Gazzetta Dello Sport, via Mail)
Sabon kocin Juventus Andrea Pirlo ya gaya wa dan wasan Argentina Gonzalo Higuain, mai shekara 32, da dan wasan Jamus Sami Khedira, mai shekara 33, cewa za su iya yin gaba a bazarar nan. (Goal)
Za a iya bayar da karin dama gaManchester United da Tottenham domin sayendan wasan gaba na Argentina Paulo Dybala, mai shekara 26, daga Juventus a bazarar nan. (Mirror)
United za ta bukaci Roma ta biya ta £20m kan dan wasan Ingila mai shekara 30 Chris Smalling, wanda ya amince a rage albashinsa domin ya tafi kungiyar da ke buga gasar Serie A. (Sun)
Napoli ta amince ta cimma yarjejeniya da Everton domin sayar da dan wasan Brazil Allan, mai shekara 29. (Express)
West Ham tana son ta karbi fiye da £80m kan dan wasan Ingila Declan Rice, mai shekara 21, a yayin da Chelseatake zawarcinsa (Times - subscription required)










