Lionel Messi: Shin ta yaya Barcelona za ta iya sauya ra'ayin ɗan kwallon da ke son raba gari da ita?

Lionel Messi

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Barin Barcelona ya gagari Lionel Messi
    • Marubuci, Awwal Ahmad Janyau
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 5

Ana ganin Messi zai iya tattaunawa da wasu ƙungiyoyi daga watan Janairu don ya fice daga Barcelona idan kwangilar shi ta kawo ƙarshe lokacin da zai iya tafiya ba wani shamaki.

Amma kafin lokacin dole sai Barcelona ta lallashi gwarzon ɗan wasan na duniya, bayan ya nuna ba ya son sake taka leda a kulub ɗin da ya shafe kuriciyarsa.

Messi ya mamaye kanun labarai a duniya bayan ya sanar da cewa ya gaji da Barcelona zai raba gari da ita. Kashin da Barcelona ta sha ci 8-2 shi ya harzuƙa Messi na rabuwa da kulub ɗinsa da ya daɗe yana cewa a nan zai yi ritaya.

Barcelona ta hana Messi tafiya har sai an biya ta kuɗin darajarsa yuro miliyan 700, matakin da Messi yake ganin yana da damar tafiya saboda wa'adin yarjejeniyar ya wuce.

Yadda aka ga babu wata murna daga magoya bayan Barcelona da Messi bayan sanar da cewa zai ci gaba da wasa a Nou Camp ya nuna cewa babu tabbas kan makomar kaftin din na Barcelona da Argentina.

Babu kuma wani martani daga ɓangaren abokan wasansa musamman kamar Suarez da Puyul da suka nuna goyon bayansa ga ɗan wasan bayan ya sanar da aniyarsa ta barin Barcelona.

Barcelona ma ba tace komi ba bayan Messi ya janye ƙudirinsa, illa hotonsa da ta wallafa da kuma ambato wasu kalaman da ya furta cewa "Zan yi iya ƙoƙarina. Soyayyata da Barcelona ba za ta taba sauyawa ba."

Kauce wa Instagram
Ya kamata a bar bayanan Instagram?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da Instagram suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Instagram da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a Instagram

Messi ya ƙauracewa atisaye ranar Asabar duk da sanar da cewa ya haƙura zai ci gaba da wasa a kulub Barcelona.

Sai dai ana ganin saboda ya ƙi zuwa gwajin korona, shi ne dallin da ya sa ya ƙauracewa fitowa horo.

Har yanzu shugaban Barcelona bai ce komi ba game da batun murabus ɗinsa, bayan a baya ya ce zai sauka idan har Messi ya fito ya bayyana cewa shi ne matsalolin kulub din.

Kuma a hirarsa da Goal, Messi ya nuna cewa akwai matsaloli a Barcelona.

Messi zai iya sauyawa?

Ko da aniyar Messi ta barin Barcelona gaskiya ce, ta yaya wannan ba zai sauya shi ba? Domin hushinsa a bayyane yake kamar yadda ya nuna.

Ana ganin shugabannin Barcelona sun tilasta masa ne ya zauna a kulub ɗin, domin idan da shugaban Barcelona Josep Maria Bartomeu yana son ya tafi da Messi ya kama gabansa.

A mahangar masharhanta kwallon ƙafa, an tilastawa Messi ci gaba da yin aikin da ba ya da imani da shi.

"Zan zauna ne saboda shugaban Barcelona ya ce dole sai an biya yuro miliyan 700, abin da kuma ba zai yiyu ba, ko kuma a bi wata hanyar ta zuwa kotu," inji Messi.

Shi kansa sabon kocin Barcelona ya nuna cewa ba shi da tabbas da abin zai iya faruwa inda ake ganin tun ɗaukar Ronald Koeman da Barcelona ta yi suka yi hannun riga da Messi.

Koeman ƙila yana ganin yadda Messi ya nuna ba ya ra'ayin wasa a Barcelona a yanzu, wani babban ƙalubale ne gare shi musamman na haɗa kan ƴan wasa da kuma burin ɗauko shi na sauya kulub ɗin.

Ko abubuwa za su sauya?

Messi

Asalin hoton, Getty Images

Har yanzu babu wata sanarwa game da ƙudirin Barcelona na tsawaita kwangilar Messi.

Rahotanni sun ambato shugaban Barcelona na cewa zai zauna ne kawai da Messi su tattauna kan yarjejeniyarsa. Ana ganin kuma wannan ba zai sauya komi ba.

Sai dai kuma abubuwa za su iya sauyawa musamman idan Bartomeu ya sha kaye a zaɓen shugabancin Barcelona. Sabon shugaba na iya kawo sauyin da zai ja ra'ayin Barcelona kamar kawo sabon kocin da Messi yake ra'ayi.

Amma kafin zaɓen Barcelona da za a yi a Maris, haƙar Messi na iya cimma ruwa domin zai iya kammala yarjejeniya da ƙungiyoyin da ke ribibinsa.

Ana ganin Barcelona za ta fuskanci ƙalubale a farkon kaka idan har Messi yana kan bakarsa.

Wataƙila kuma magoya bayan Barcelona su taimaka a fili su dinga rera wa gwaninsu waƙa ta yabo da janyo ra'ayinsa don ya dawo da soyayyar da ta rikiɗe ta koma ƙiyayya ga Barcelona.

Za a ɗauki lokaci kafin abubuwa su daidaita tsakanin Messi da Barcelona amma ya dogara da yadda Barcelona ta karrama shi ba ta wulaƙanta shi ba.

Ganiyar Messi raguwa ta ke yi ko ƙaruwa?

Lionel Messi with his six Ballon d'Or trophies

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sau shida Lionel Messi na lashe Ballon d'Or

Tarihin ƙwallon ƙafa ba zai taɓa mantawa da Messi ba, Messi ya lashe kyautar gwarzon ɗan wasan duniya sau shida - Tarihin da babu wanda ya kafa.

Amma yanzu ana ganin ɗan wasan ba ya kan ganiyarsa.

Messi a kaka. . Wasanninsa a La Liga da Champions League idan aka haɗa.

A karon farko Messi ya kammala kaka ba kofi tun 2008. Kuma shekaru biyar bai lashe kofin zakarun Turai ba.

Kaka uku a jere ana yi wa Messi da Barcelona wulaƙanci a Champions League musamman abin da aka gani a Roma da Liverpool da kuma Bayern Munich.

Irin yawan kuɗin da Barcelona ta aza a matsayin darajar Messi, wanda ya hana shi barin kulub ɗin, wasu na ganin yanzu darajarsa ba ta kai can ba musamman yadda ake ganin ba ya kan ganiyarsa kamar shekarun baya?

Messi mai shekara 33 shi ya fi kowa yawan zira kwallaye a La Liga a kakar da aka kammala, amma kuma kaka ce da bai ci kwallaye ba da yawa kamar yadda ya saba.

Shin har yanzu babu kamar Messi?

Messi shi ya fi cin kwallaye a tarihin Barcelona da kwallaye 634 a wasanni 731, kuma wanda ya fi yawan cin kwallaye a tarihin La Liga a haskawa 485.

Messi ya taba cin kwallaye 91 a Barcelona da Argentna a 2012.

Messi ya lashe La liga 10 da kofin Zakarun Turai hudu, shi ya fi cin kwallaye a tarihin Argentina inda ya ci kwallaye 70 a wasanni 138.

Sau bakwai Messi na lashe takalmin zinari a matsayin wanda ya fi yawan zirara kwallo a raga.

"Kakar da ta gabata ta nuna cewa ganiyar Messi na raguwa," inji Andy West dan jarida kuma mai sharhi kan ƙwallon ƙafa a Spain wanda ya rubuta littafi game da Messi.

"Idan dai yanzu batun cin kwallaye ne yanzu wasu sun sha gaban Messi," in ji shi.

Yawan ƙwallaye da taimakawa a ci a 2019-20 (Dukkanin wasanni). . Ƴan wasan da manyan lig na Turai 5 - Bundesliga, Premier League, La Liga, Serie A da Ligue 1.

Robert Lewandowski na Bayern Munich shi ya fi kowa cin kwallaye a raga a bana inda ya ci 55.

Kuma a Seria A, ga Ciro Immobile da Cristiano Ronaldo da Romelu Lukaku da kuma ɗan wasan gaba na RB Leipzig Timo Werner yanzu da ke Chelsea, dukkaninsu sun fi cin kwallaye fiye da Messi.

Raheem Sterling na Manchester City ma ya ci kwallaye 31 a dukkanin wasannin da ya buga a kakar da aka kammala.

Ƴan wasan da suka fi cin kwallo a raga a Turai a kakar 2019-20 . . Ƴan wasan manyan lig 5 na Turai - Bundesliga, Premier, La Liga, Serie A da Ligue 1.

Sai dai Messi ne na biyu tsakanin ƴan wasan da suka fi taimakawa a ci kwallo a kakar da aka kammala inda ya taimakawa aka ci kwallo 56.

Haka kuma a dukkanin wasanninsa, Messi ya fi kowa yawan yanke a manyan lig na Turai guda biyar.

Amma har yanzu ana muharawa kan ko Messi yana cikin manyan ƴan kwallo a duniya, duk da ana ganin Lewandowski yanzu ya sha gaban kowa a kakar 2019-20.

Akwai kuma muhawarar da ake yi ko zai iya dawo wa kan ganiyarsa idan har ya sauya kulub saɓanin Barcelona da ake ganin abubuwa sun taɓarɓare.