Jose Maria Bartomeu: Shugaban Barcelona zai fuskanci ƙuri'ar yankan ƙauna

Lionel Messi (right) has had a public falling out with Bartomeu (left)

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Lionel Messi (dama) ya sha sukar shugaban Bartomeu (hagu)

Za a jefa ƙuri'ar raba-gardama kan shugaban Barcelona Josep Maria Bartomeu sakamakon fafutukar da wasu ke yi wajen ganin an sauke shi daga kan mukamin nasa.

Bartomeu, wanda ya zama shugaban Barca a 2014, yana fuskantar matsin lamba, musamman bayan dan wasan kungiyar Lionel Messi ya bayyana aniyarsa ta barin kungiyar a watan Agusta.

An nemi sauke Bartomeu daga kan mukaminsa kwana guda bayan Messi ya bukaci barin kungiyar.

A halin da ake ciki mutum 20,731 ne suka sanya hannu a takardar da ta bukaci ya sauka daga kan mukaminsa, kuma hakan na nufin Bartomeu na iya fuskantar ƙuri'ar yankan ƙauna.

Ana bukatar mutum 16,500 su nemi ya sauka daga kan mukaminsa kuma da zarar an tabbatar da wannan adadi, shugaban na Barcelona mai shekara 57 zai fuskanci ƙuri'ar yankan ƙauna cikin wata uku.

Mambobin kungiyar guda 150,000 ke da alhakin jefa ƙuri'ar yankan ƙauna kuma idan kashi 66.5 suka yarda ya sauka to dole ya ajiye mukaminsa.

Bartomeu zai sauka a watan Maris, idan ya kammala wa'adi na biyu na karshe a matsayin shugaban kungiyar.

Sai dai da alama zai zama shugaban Barcelona na uku da zai fuskanci ƙuri'ar yankan ƙauna bayan Josep Lluis Nunez a 1998 da Joan Laporta a 2008, kodayake dukkan su biyun sun sha da ƙyar.

Messi ya amince ya ci gaba da zama a kungiyar sai dai zaman tsamar da ake yi da Bartomeu yana ci gaba da ƙamari tun daga shekarar da ta wuce sakamakon rashin kudi da kuma rashin tagomashin kungiyar abin da ya sa ba su dauki ko da babban kofi daya ba a kakar da ta wuce.

A gefe guda, tsohon kocin kungiyar Quique Setien da mataimakansa uku sun sanar ranar Alhamis cewa za su gurfanar da kungiyar a kotu saboda gaza cika sharudan kwangilarsu inda aka kore su a watan jiya.

Sun yi ikirarin cewa sun samu takardar da ta dakatar da ta kore su daga ranar 16 ga watan Satumba, duk da cewa an sallame su ranar 17 ga watan Agusta.

Setien ya ce ba a ba shi kudin sallama ba kuma takardar da aka tura masa ranar Laraba "ta nuna aniyar kungiyar karara cewa ba ta da niyyar yin biyayya ga tsarin kwangilar da muka sanya wa hannu ranar 14 ga watan Janairu na 2020."