Manchester United tana son ɗauko Willian, Everton tana zawarcin Allan

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United ta tuntubi wakilin Willian domin tattaunawa kan karbo dan wasan mai shekara 31 dan kasar Brazil, wanda kwangilarsa za a kare a Chelsea wannan bazarar. (France Football - in French)
KocinEverton Carlo Ancelotti ya soma tattaunawa da dan wasan tsohuwar kungiyarsa Napoli Allan dan shekara 29, dan kasar Portugal. (Express)
Kazalika Ancelotti ya yi yunkurin dauko dan wasan Paris St-Germain da Brazil mai shekara 35 Thiago Silva da zarar kwangilarsa ta kare a bazarar nan. (Express)
Dangantakar Gareth Bale da kocin Real Madrid Zinedine Zidane ta yi tsamin da ba za ta gyaru ba, ko da yake dan wasan na Wales mai shekara 30 yana cike da farin ciki a kungiyar ta Spaniya. (Marca)
Har yanzu babu tabbas kan makomar Jadon Sancho a Borussia Dortmund bayan babban kocin kungiyar Lucien Favre ya amince cewa dan wasan na Ingila mai shekara 20 yana cikin 'yan wasan da za su iya barin kungiyar a wannan bazarar. (Sky Sports)
Kocin RB Leipzig Julian Nagelsmann ya dage cewa Timo Werner, mai shekara 24, yana cikin 'yan wasan da suke son ya buga musu Gasar Zakarun Turai, duk da cewa dan wasan na Jamus ya kulla yarjejeniya da Chelsea. (Mirror)
Leicester City ta bi sahun Manchester United a kokarin dauko dan wasan Lyon dan kasar Faransa mai shekara 23 Moussa Dembele. (France Football, via Leicestershire Live)
YunkurinChelsea na dauko dan wasan Bayer LeverkusenKai Havertz ya samu tagomashi bayan kungiyarsa ta ce ba za ta yi 'kafar-ungulu' ba idan ya nemi barinta, bayan dan wasan mai shekara 21 dan kasar Jamus ya ce yana son komawa wata kungiyar. (Kolner Stadt-Anzeiger - in German)











