Leicester da Crystal Palace na fafatawa don ɗauko Tarkowski, Man City ta sanya ido kan Hakimi

Asalin hoton, Getty Images
Leicester City tana gogayya da Crystal Palace a yunkurin dauko dan wasan Burnley da Ingila James Tarkowski, mai shekara 27. (Mirror)
A wannan makon ne Timo Werner zai kammala komawa Chelsea daga RB Leipzig ahukumance, a yayin da wa'adin sayar da dan wasan na Jamus mai shekara 24 a kan £53m zai zo karshe yau. (Evening Standard)
Juventus tana son dauko dan wasan Chelsea mai shekara 28 dan kasar Italiya Jorginho da dan wasan Spaniya Marcos Alonso, mai shekara 29. (Express)
Manchester City tana sanya ido kan dan wasan Real Madrid da Morocco Achraf Hakimi. A halin da ake ciki dan wasan mai shekara 21 yana zaman aro a Borussia Dortmund. (AS, via Sun)
Chelsea ta soma tattaunawa da dan wasan Brentford mai shekara 24 dan kasar Algeria Said Benrahma. (RMC, via Express)
Tattaunawar da Chelsea take yi da Benrahma wani koma-baya ne ga Aston Villa, wacce aka kwashe fiye da shekara daya ana sa ran za ta dauko shi. (Birmingham Live)
Tsohon dan wasan Netherlands Ronald de Boer ya ce dan wasan tsakiya na Ajax wanda kasarsu daya Donny van de Beek, mai shekara 23, zai fi son komawa Real Madrid a kan Manchester United. (Marca)
Nice za ta nemi sayen dan wasan Everton da Faransa Morgan Schneiderlin, mai shekara 30, a kan £2m wannan makon. (Mail)
Kocin Tottenham Jose Mourinho yana son karbo aron golan Paris St-Germain da Brazil Thiago Silva, mai shekara 35, a bazara. (Sun)
Rahotanni sun ce a shirye Arsenal take ta bai wa dan wasan Atletico Madrid Thomas Partey alawus ninki uku a yunkurin da take yi na dauko dan kasar Ghana mai shekara 27. (Goal, via Mirror)
Norwich ta kusa dauko dan wasanSunderland mai shekara 18 Bali Mumba. (Mail)











