Messi ya ci kwallo na 699 a karawa da Leganes

Asalin hoton, Getty Images
Barcelona ta ci gaba da zama ta daya a kan teburin La Liga, bayan da ta doke Leganes da ci 2-0 a wasan mako na 29 da suka kara ranar Talata a Camp Nou.
Matashin dan wasa dan kasar Guinea-Bissau Ansu Fati shi ne ya fara cin kwallo daga baya Messi ya kara na biyu a bugun fenariri.
Kyaftin din Barcelona ya ci kwallo na 699 a Barca da tawagar Argentina a bugun fenariti, bayan da Ruben Perez ya yi masa keta a cikin da'irar Leganes.
Yanzu Barcelona ta bai wa Real tazarar maki biyar, sai dai kuma za ta buga da Valencia ranar Alhamis kila tazarar ya koma biyu kacal.
Ansu Fati, mai shekara 17 wanda ya ci kwallo na biyar a La Liga ya kafa tarihin mai karancin shekaru na biyu da ya buga wa Barcelona kwallo a kungiyar.
Ya kuma kafa wannan tarihin ranar 25 ga watan Agusta a wasan da Barca ta doke Real Betis 5-2 a lokacin yana da shekara 16 da kwana 298.
Iyayensa sun koma Spaniya a lokacin da Fati ke da shekara shida, ya kuma fara buga tamaula a karamar kungiyar tun daga 2012.







