Real Madrid ta ci gaba da zama ta biyu a teburin La Liga

Real Madrid

Asalin hoton, Getty Images

Real Madrid ta ci gaba da zama ta biyu a teburin La Liga, bayan da ta doke Eibar 3-1 a wasan mako na 28 da suka kara ranar Lahadi.

Karon farko da Real Madrid ta buga gasar tun cikin watan Maris, bayan da aka dakatar da wasannin don gudun yada cutar korona.

Real wadda ta karbi bakuncin Eibar ta ci kwallo uku tun kan hutu ta hannun Toni Kroos da Sergio Ramos da kuma Marcelo Vieira Da Silva.

Eibar wadda take ta 16 a kasan teburi ta zare kwallo daya ta hannun Pedro Bigas a minti na 15 da ci gaba da fafatawar zagaye na biyu.

Real Madrid ta hada maki 59 tana nan a matakinta na biyu, biye da Barcelona wadda take kan teburi da maki 61.

Wannan ne wasa na 200 da kocin Real Madrid, Zinedine Zidane ya ja ragamar kungiyar a matsayin koci.

Real Madrid za ta karbi bakuncin Valencia a wasan mako na 29 ranar Alhamis, yayin da Barcelona za ta kece raini da Leganes ranar Talata a Camp Nou.