Messi ya ci kwallo 20 ko fiye da haka a kaka 12 a jere a La Liga

Lionel Messi

Asalin hoton, Getty Images

Ranar Alhamis aka ci gaba da gasar La Liga karawar mako na 28, tun bayan da aka dakatar da wasannin cikin watan Maris saboda bullar cutar korona.

Ranar Asabar Barcelona ta ziyarci Real Mallorca ta kuma doke ta da ci 4-0, kuma Messi ne ya ci na karshe na kuma 20 a La Liga ta bana.

Shi ne kuma ya bai wa Braithwaite da Jordi Alba kwallayen da suka zura a raga, kafin daga baya shima ya ci na sa.

Kawo yanzu kyaftin din Argentina ya ci kwallo 20 a gasar La Liga ta bana kuma kakar tamaula 12 a jere kenan yana wannan bajintar ko fiye da haka..

Babu dan wasan da ya yi haka a tarihi, za kuma a dauki lokaci kan a samu wanda zai yi wannan bajintar a harkar kwallon kafa.

A kakar 2008-09 ya fara da zura kwallo 20 ko fiye da haka a tarihi har zuwa yanzu, kuma a gasar 2011-12 ya ci kwallo 50 a raga.

Duk da Barcelona ce kan gaba a teburin La Liga, Messi shi ne kan gaba a zura kwallaye a wasannin bana.

Haka kuma shi ne kan gaba wajen bayar da kwallo a zura a raga wanda ya yi wannan bajintar sau 14 ya kuma ci kwallo biyu a Champions League da wasu biyun a Copa del Rey da guda daya a Spanish Super Cup a bana.