La Liga: Wadanda za su buga wa Real Madrid wasa da Eibar

Asalin hoton, Getty Images
A daren nan Real Madrid za ta karbi bakuncin Eibar a wasan mako na 28 a gasar cin kofin La Liga na bana.
Ranar Alhamis aka dawo ci gaba da gasar Shekarar nan, bayan da aka dakatar da wasanni cikin watan Maris saboda bullar cutar korona.
Real Madrid wadda ta yi wasa 27 tana mataki na biyu da tazarar maki biyar tsakaninta da Barcelona.
Barca ta buga wasan mako na 28 ranar Asabar, wadda ta je ta doke Real Mallorca da ci 4-0.
Kocin Real Madrid zai ja ragamar kungiyar wasa na 200 a karawa da Eibar, kuma tuni ya sanar da sunayen 'yan kwallo 23 da za su buga masa wasan.
'Yan kwallon da za su buga wa Real wasan Eibar:
Masu tsaron raga: Courtois da Areola da kuma Altube.
Masu tsaron baya: Carvajal da Militão da Ramos da Varane da Marcelo da Mendy da kuma Javi Hernández.
Masu wasan tsakiya: Kroos da Modric da Isco da Casemiro da Valverde da kuma James.
Masu buga gaba: Hazard da Benzema da Bale da Asensio da Brahim da Vinicius Jr da kuma Rodrygo.










